Mike Tyson bai yi da-na-sanin yin dambe da Jake Paul ba

Shararren tsohon dan wasan damben duniya Mike Tyson ya jaddada cewa bai yi da-na-sani ba, bayan kashin da ya sha a hannun Jake Paul.  Mai shekaru 58 a duniya, Tyson ya dambance da matashi Paul dan shekaru 27 a duniya kacal, inda aka fitar da shi a turmi na takwas a filin wasa na AT&T a birnin Texas na Amurka, Paul da ya kasance a baya yana watsa bayanai a shafin YouTube kafin ya koma dambe, ya lashe gasar da maki 80 da 72. Ssai 79 da 73 sai kuma 79-73 a kan dan damben ajin masu nauyin da ya yi murabus a  2005.

Ko da aka tambaye shi kan yadda ya ji jim kadan bayan kammala damben Tyson ya ce: "Matukar farin ciki? E. Ban yi mamaki ba, na san kwararren dan wasa ne. Na san ya shirya, sai dai ni ma na zo ne in dambance. Na yi ne ba domin na burge kowa ba, na yi saboda kaina. Ni ba irin mutanen nan ne da suka damu da abin da duniya za ta fada a kansu ba, kawai ina cikin farin ciki."  

Shi kuwa a nasa bangaren matashin dan wasa Jake Paul cewa ya yi: "Abu na farko, Mike Tyson abin girmamawa ne a gare ni. Dole mu jinjina masa, shi gwarzo ne shahararre. Na samu kwarin gwiwa daga gare shi, ba domin shi ba da ban samu kaina a nan ba. Wannan mutumin abin koyi ne, girmamawa ce yin dambe da shi. Gaskiya shi ne mutum mafi dauriya da juriya a duniya da na sani, na ji dadi kwarai damben ya tafi yadda na tsammata."

Kalaman batanci sun shafa wa Rodrigo kashin kaji

Rodrigo Bentancur ya yi kalaman batanci ga 'yan Koriya ta Kudu ciki har da Son Heung-min, Rodrigo Bentancur ya yi kalaman batanci ga 'yan Koriya ta Kudu ciki har da Son Heung-min, Hoto: Sebastian Frej/IMAGO

An dakatar da dan wasan tsakiya na Uruguay Rodrigo Bentancur Colmán daga buga wasanni har bakwai, bayan da aka kama shi da laifin yin wasu kalaman batanci ga 'yan Koriya ta Kudu da aka alakanta su da wani takwarsa a kungiyarsu ta Tottenham Son Heung-min da ya kasance dan Koriya ta Kudun. Hukumar Kula da Wasannin Kwallon Kafa ta Ingila ce ta sanar da hakan, inda ta ce kwamitin da ta kafa mai zaman kansa domin gudanar da bincike kan kalaman batancin da Rodrigo Bentancur ya yi a kan Son Heung-min ya kuma ci tararsa Fam din Ingila dubu 100 kwatankwacin dalar Amurka dubu126. 

Kosovo ta halarci gasar Nations League a makare

Mai horas da 'yan wasan Kosovo Franco Foda ya nunar da cewa hukuncin da Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Kasashen Turai UEFA ka iya dauka a kan 'yan wasan kasarsa sakamakon barin filin wasa a makare yayin gasar Nations League da suka fafata da Romaniya bayan zargin magoya bayan Romaniya da muzanta su, abu ne da ba shi da muhimmanci a gare shi, tare da mara wa 'yan wasansa baya. Ya kara da cewa tsayawar da suka yi, wani mataki ne na aike sako ga magoya baya kan abun da aka aikata musu ba shi da gurbi a filin wasa. A cewarsa filin wasa waje ne na girmama juna, domin hakan ya fi muhimmanci fiye da samun nasara. Akwai yiwuwar hukumar ta UEFA da ke gudanar da bincike kan lamarin da ake sa ran za ta yanke hukunci cikin wannan makon, ka iya bai wa Romaniya maki uku a wasan da suka tashi canjaras babu ci tsakaninsu da Kosovo.

Talla

NBA ta ci tarar wani dan kwallon kwando na Charlotte 

NBA ta ci tarar mai tsaron raga na kungiyar kwallon kwando ta CharlotteNBA ta ci tarar mai tsaron raga na kungiyar kwallon kwando ta CharlotteHoto: Eibner Europa/imago images

Hukumar Kula da Wasannin Kwallon Kwando ta Amurka wato NBA ta ci tarar mai tsaron raga na kungiyar kwallon kwando ta Charlotte Hornets LaMelo LaFrance Ball dalar Amurka dubu 100, bayan da ya yi wasu kalaman batanci kan masu auren jinsi. Rahotanni sun nunar da cewa, Ball ya yi wadannan kalaman ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin jim kadan bayan kammala wasa kan tambayar da aka yi masa dangane da kare wani bugu da ya kasance na karshe da dan wasan Milwaukee Bucks Giannis Antetokounmpo yayi a wasan da Charlotte ta samu nasara da ci 115 da 114 a kan 'yan wasan na Bucks.

Aski ya fara zuwa gaban goshui a gasar CONCACAF

An fara wasan kusa-kusa da na karshe, watau Quarter-Finals na bana, na cin Kofin Kwallon Kafa na Gamaiyar Kasashen Amurka Ta Arewa da Tsakiya da kuma na Caribbean da ake kira CONCACAF a takaice, yayin da a fagen Kwallon Kwando kuma, tauraruwar dan wasa Victor Wembanyama take ci gaba da haskawa sosai.

Rafael Nadal na ci gaba da shiga kaunun labarai

Rafael Nadal na shirin fafata wasan Davis Cup a  MalagaRafael Nadal na shirin fafata wasan Davis Cup a  MalagaHoto: Pau Barrena/AFP/Getty Images

Fitaccen dan wasan kwallon Tennis na duniya Rafael Nadal ya bayyana cewa ba zai mayar da hankali kan tunanin yin murabus ba, a yayin da suke shirin fafata wasan Davis Cup a  Malaga. Mai shekaru 38 a duniya, ya ce zai mayar da hankali ne kawai wajen taimakon kasarsa Spaniya ta lashe kofin a gasar da za a fafata a wannan mako. Nadal zai bayyana ritayarsa daga wasan da ya kwashe sama da shekaru 20 yana fafatawa, wanda ya ba shi damar lashe kambun manyan wasannin Tennis wato Grand Slam har sau 22 da kuma na French Open har sau 14. A cewarsa wannan shi ne makonsa na karshe da zai buga wasa ga kungiyar kasarsa ta Spaniya, saboda haka abin da zai mayar da hankali a kai shi ne taimaka musu su lashe gasar. 


News Source:   dw.com