Jarumin barkwanci a masana'antar shirya fina-finai ta Nollywood John Okafor, da aka fi sani da Mr. Ibu ya rasu.
WASHINGTON DC - Ya mutu ne sakamakon bugun zuciya bayan da kimanin mako guda daya gabata aka sake garzayawa da shi zuwa wani asibitin birnin Legas sanadiyar sake tasowar larurar da yake fama da ita.
Wani na kusa da iyalan mamacin ya shaidawa tashar talabijin na Channels cewa fitaccen jarumin ya rasu ne da tsakar ranar Asabar din nan bayan da aka mayar da shi sashen kulawar musamman na asibitin Evercare dake unguwar Lekki a 'yan kwanakin da suka gabata.
Ya rasu ne sakamakon bugun zuciya bayan da ciwon zuciyarsa ya sake tashi kimanin mako guda daya gabata, abinda ya sabbaba garzayawa da shi zuwa asibitin dake dake jihar Legas.
Haka shima, Shugaban Kungiyar Jaruman fina-finai ta Najeriya, Emeka Rolla, ya tabbatar da mutuwar jarumin.
A shekarar data gabata, an yankewa jarumin kafa ta hanyar tiyata bayan daya nemi taimako da addu'o'i daga masoyansa.
Rasuwar Mr. Ibu na zuwa ne bayan rasuwar abokin aikinsa Tolani Quadri Oyebamiji, wanda aka fi sani da Sisi Quadri wanda ya mutu a jiya Juma'a kuma aka yi jana'izarshi a yau asabar a mahaifarsa ta Iwo, dake jihar Osun.