Babban daraktan hukumar ta NCDC Jide Idris, ya ce duk da cutar ba ta tsananta matuka a ƙasar ba amma abin damuwa ne lura da yadda ta ke matsayin barazana ga lafiya.
A jawabin da ya gabatar, Jide Idris ya shawarci al'ummar Najeriya da su ɗauki matakan kariya daga cutar baya ga gaggauta ziyartar asibiti don gwaji da zarar an samu alamomin cutar da kuma bayar da rahoton duk wanda aka samu da cutar don daƙile yaɗuwarta.
Kasashen duniya da dama sun fara daukar matakai don dakile bullar cutar a tsakanin al’ummarsu, musamman bayan ganin ɓullarta a Pakistan da ta samu mutum biyu da suka harbu da kuma Sweden da ita ta sanar da ɓullar cutar tun a ranar Alhamis.
Tuni dai hukumar WHO ta roƙi kamfanonin sarrafa magunguna da su yi azama wajen wadata ƙasashe da rigakafin cutar ta ƙyandar biri tun gabanin ta tsananta.
A farkon makon nan ne WHO ta ayyana dokar ta ɓaci kan cutar wadda tun farko aka samu ɓullarta a Jamhuriyyar Demokraɗiyyar Congo kuma kawo yanzu ta ke ci gaba da kisan jama'a.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI