Najeriyar na sayar da makaman da ta ke ƙerawa ga tarin ƙasashe - Matawalle

Najeriyar na sayar da makaman da ta ke ƙerawa ga tarin ƙasashe - Matawalle

A jawabinsa jiya Litinin gaban taron bikin cika shekaru 60 da kafa ma’aikatar ƙera makaman, ministan tsaron Najeriyar Bello Matawalle ya bayyana cewa, galibin ƙasashen Afrika a yanzu na sayen makamai daga kamfanin na DICON wanda ke ƙarƙashin ma’aikatar tsaro ne don samar da tsaro a ƙasashensu.

A shekarar 1964 ne aka samar da kamfanin na DICON da nufin samar da makaman da Najeriya ke buƙata don rage dogaro da shigo da makamai daga ƙetare.

Sai dai har zuwa yanzu cinikayyar makaman da Najeriyar ke yi ta ta’allaƙa ne kacokan a hada-hadar ƙetare musamman a halin da ake ciki na yaƙi da matsalolin tsaro daga ƴan ta’adda da ƴan bindiga da sauran ƙalubalen tsaron da ƙasar ta yammacin Afrika ke fama da su.

Kafin sabuwar dokar dai DICON na da damar samar da makaman da za a iya amfani da su a cikin gida ne kaɗai sai dai daga bisani Najeriyar ta sahalewa kamfanin ƙera makaman da za a sayarwa ƙasashen maƙwabta don samun kuɗaɗen shigar tafiyar da harkokin ƙasar lura da yadda ake fama da ƙamfarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)