Masu tarawa Najeriya ƙuɗaɗen shiga sun ƙi sanya sama N4.1tn asusun gwamnati - FAAC

Masu tarawa Najeriya ƙuɗaɗen shiga sun ƙi sanya sama N4.1tn asusun gwamnati - FAAC

Hakan na ƙunshe ne cikin wani rahoto da kwamitin rabon arzikin ƙasa ya bayyana yayin wani taro ranar Talalata a Abuja, wanda shugaban tattara kudaden shiga, rabo da kuma kasafin kudi, Mohammed Shehu ya sanyawa hannu.

Alkaluman sun nuna cewar, kamfanin man fetur na NNPCL  ya rike N940.62bn; Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya nada dala miliyan 23.81 da N1.94tn.

Hukumar tara haraji ta tarayya da kuma NNPC na da kudaden kadai na rike da bashin dala miliyan 141.25 da kuma N1.04tn, yayin da ma’aikatar ci gaban ma’adanai da babban bankin Najeriya ke da N48.75m.

Watanni biyu da suka gabata, rahotanni sun bayyana cewar, gwamnati na iya yin asarar sama da N3tn idan hukumomin samar da kudaden shiga ba su shigar da ƙudaden baitul malin gwamnati ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)