Ƴan bindiga sun kashe mutane kusan dubu 25 cikin shekaru 5 a Najeriya - Rahoto

Ƴan bindiga sun kashe mutane kusan dubu 25 cikin shekaru 5 a Najeriya - Rahoto

Global Rights ta bayyana cewa cikin wannan adadi na mutum kusan dubu 25 da ‘yan bindigar suka kashe a Najeriya har da manoma dubu 1 da 356 galibinsu daga yankin arewacin Najeriya tsakanin shekarar 2020 zuwa 2024.

A cewar ƙungiyar wannan matsalar ta ruɓanya tsakanin watan Yulin shekarar 2023 zuwa Yunin shekarar 2024.

Kungiyar Global Rights ta ce matsalar ta fi kamari a yankin arewacin Najeriya, mai fama da matsalolin tsaro.

A cewar Global Rights aƙalla mutane miliyan 3 da dubu 400 yanzu haka suka gujewa muhallinsu da garuruwansu saboda wannan tashin hankalin.

Daraktar kungiyar ta Global Rights a Najeriya Abiodun Bayeiwu ta ce akwai 'yan Najeriya sama da dubu 100 da yanzu haka ke gudun hijira a ƙasashen maƙwabtaka.

Bayeiwu ta kara da cewar a yankin arewacin Najeriya akwai akalla mutane dubu 457 da tashe tashen hankula suka tilastawa barin muhallinsu, adadin da ya ribanya na shekarar 2022 da ƙasar ta gani.

Aƙaluman da ƙungiyar ta fitar ya zayyana wasu jihohin arewacin Najeriyar 5 mafiya fama da tashe-tashen hankula da matsalolin tsaro ciki har da ayyukan masu garkuwa da mutane waɗanda suka ƙunshi jihar Filato da Borno da Benue da Kaduna da kuma Zamfara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)