Ademola Lookman, William Troost-Ekong, Paul Onuachu da Asisat Oshoala su ne ‘yan Najeriyar da suka shiga jerin ‘yan wasan da aka tsamo don neman kambun a matakai daban-daban.
Washington D.C. —Hukumar Kwallon Kafata Duniya FIFA ta fitar da jerin sunayen ‘yan wasan da suke takarar neman kyautar gwarazan FIFA na bana.
‘Yan Najeriya hudu ne suka samu shiga jerin sunayen a matakai daban-daban da suka hada da gwanayen zura kwallo, masu tsaron gida, masu tsaron raga, masu horarwa da sauransu.
Ademola Lookman, William Troost-Ekong, Paul Onuachu da Asisat Oshoala su ne ‘yan Najeriyar da suka shiga jerin ‘yan wasan da aka tsamo don neman kambun a matakai daban-daban.
Lookman wanda ya zo na 14 a neman kyautar Ballon d’Or zai kara da ‘yan wasa irinsu Vinicius Junior, Lamine Yamal, Bukayo Saka, Erling Haaland, Lionel Messi da Cristiano Ronaldo.
Kyaftin din Najeriya Troost-Ekong zai fafata wajen neman kambun iya tsaron gida da ‘yan wasa irinsu William Saliba, Manuel Akanji, Antoni Rudiger da Dani Carvajal.
Ita kuwa Oshoala an zabe ta ne wajen neman sabuwar kyautar “Marta Award” a matsayin wacce ta kware wajen iya zura kwallo a bangaren mata.