Tottenham ta tashi zuwa matsayi na 8 kuma ta yi nasara a wasanni hudu a jere a dukkan gasar.
Washington D.C. —Manchester United ta sha kashi a hannun Tottenham a gasar Premier League.
An doke ta da 3-0 a Old Trafford ranar Lahadi, kuma an kori kaftin dinta, Bruno Fernandes, a ci gaba da mummunan fara wannan kakar wasa.
Kwallaye daga Brennan Johnson, Dejan Kulusevski, da Dominic Solanke sun sa United ta sha kashi na uku a gasar wannan kakar, inda hakan ya bar tawagar Erik ten Hag a matsayi na 12 a teburin gasar.
United ta samu nasara sau daya tak a wasanninta biyar da ta buga a gasar.
Tottenham ta tashi zuwa matsayi na 8 kuma ta yi nasara a wasanni hudu a jere a dukkan gasar.
United ta gaza samun nasara a wasanni uku da ta buga a baya-bayan nan a dukkan gasanni.
A dayan wasan Premier League na ranar Lahadi, Aston Villa ta tashi 2-2 da Ipswich, inda ta rasa damar da za ta yi daidai da maki na farko tare da Liverpool.