Wasanni: Makomar Dortmund a Bundesliga

Fafatawar da aka yi tsakanin Bayer Leverkusen da ke a matsayi na biyu na Bundesliga da  Bayern Munich ya dauki hankali sosai, sai dai duk da damarmaki masu yawa da 'yan wasan Leverkusen suka samu tare da nasarar mamaye Bayern Munich an tashin wasan canjaras babu ci. Wannan lamari dai, ya bakanta ran mai horas da 'yan wansa na Leverkusen Xabi Alonso ganin irin bajintar da 'yan wasansa na Leverkusen suka nuna. Alonso ya ce yana ganin sun yi duk abin da ya dace domin samun nasara a wannan wasa, amma dai sun rasa samun nutsuwa. Wannan sakamakon bai taimaki Leverkusen ba, tun da har yanzu zakaran kwallon kafar na Jamus na da ratar maki takwas tsakaninta da Bayern Munich. Hasali ma wannan tazarar za ta yi wuyar cikewa kafin karshen kakar wasa ta bana.

Bundesliga | Holstein Kiel | Eintracht FrankfurtGumurzu tsakanin Eintracht Frankfurt da Holstein KielHoto: Frank Molter/dpa/picture alliance

Ita kuwa Frankfurt tana ci gaba da mannewa a matsayi na uku na teburin na Bundesliga, bayan da ta doke Holstein Kiel da ci uku da daya ta kuma fadada tazararta da kungiyoyin da ke biya mata baya. A nata bangaren RB Leipzig da ke a matsayi na hudu na cikin rudani, bayan da ta tashicanjaras babu ci a karawarta da Augsburg. Hasali ma dai, kungiyoyin Freiburg da Mainz suna kusantar Leipzig a yawan maki, bayan da suka yi nasarar doke St. Pauli da Heindenheim a karshen mako. Ita kuwa Borussia Dortmund ta kasance a halin gaba kura baya siyaki, bayan da ta sha kashi da ci biyu da nema a gidan 'yar baya ga dangi VfL Bochum. Wannan lamarin ya janyo kungiyar ci gaba da zama daram, a matsayi na 11. Amma ga Bochum wannan nasarar tana da daraja, domin ta tashi daga matsayin karshe zuwa na 17 kuma tana gogayya da Heindenheim a yawan maki.

Ingila | Manchester City | Premier League | Omar Marmoushsabon dan wasan Manchester City Omar Marmoush ya yi rawar gani, a karshen makoHoto: Mark Cosgrove/News Images/Avalon/picture alliance

A Ingila kuwa Omar Marmoush na Manchester united ya yi nasarar kafa murhun kwallaye, inda ya zura wa Newcastle kwallaye uku rigis a mintuna 14 kacal. Da ma dai dan kasar Masar wanda da ya koma City shekaru biyu da suka gabata bai taba cin kwallo ba, lamarin da ya faranta wa mai horas da 'yan wasa Pep Guardiola rai. Amma dai duk haka Manchester City ta kasance a matsayi na hudu na gasar Premier, yayin da abokiyar gabarta Manchester United ta sha kashi a hannun Tottenham da ci daya mai ban haushi a wasan mako na 25 a Premier ta Ingila abin da ya jefa ta a matsayi na 15 da maki 29. Amma dai a bangarenta, Liverpool ta su Mohamed Salah da ta samu nasara a kan Wolves tana ci gaba da jan zarenta a samen teburin da maki 60. Ita kuwa Arsenal tana biya mata baya da maki 53, yayin da Nottingham Forest ke a matsayi na uku da maki 47.

Spaniya | La liga | Real Madrid | Jude BellinghamDan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Jude Bellingham ya karbi jan katiHoto: Ryan Pierse/Getty Images

A Spain kuwa, rashin mutumci da ake zargin dan wasan Real Madrid Jude Bellingham da aikatawa bisa jan kati a wasan da aka tashi kunnen doki daya da daya da Osasuna ne ya fi daukar hankali. Shi dai dan wasan tawagar Ingila mai shekara 21, ya danganta lamarin da ''rashin fahimta'' kuma ya ce bai ci mutumcin alkalin wasa ta hanyar ambata kalamai marasa kan gado ba. MAi horas da 'yan wasan Madrid din Carlo Ancelotti ya goyi bayan hakan, yayin da mai horas da Barcelona ya ce rashin mutumci ne. An bai wa Bellingham jan kati ne a mintuna na 39,  bayan da ya fada wa alkalin wasa Jose Luis Manuera Montero kalaman da ba su dace ba. Sai dai duk da wannan tuntube da ta yi a gaban Osasuna, Madrid ce ke kan gaba a gasar La liga ta Spaniya da maki 51 yayin da daya kungiyar ta Madrid wato Atletico Madrid ke bi mata baya da maki 50 kana Barcelona ta su Lamine Yamal ke a matsayi na uku da mai 48. A nahiyar Afirka kuwa, tawagogin kasashe da dama sun bayyana kaurace wa tseren keke na Ruwanda da zai gudana daga ranar 23 ga Fabarairun 2025 sakamakon katsaladan da kasar ke yi a harkokin tawaye na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango abin kuma da zai rage armashin gasar. Babbar tawagar tseren keke ta  Beljiyam mai suna Soudal Quick-Step ta yanke shawarar janyewa daga tseren keken, saboda barazana da 'yan tserenta za su iya fuskanta a kusa da iyakar Ruwandan da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. Daya daga cikin matakan tseren keken dai zai bi ta Rubavu, wani gari mai nisan kilomita 15 daga Goma da ke fama da rikicin tawaye. Duk da rikici da take fama da shi da makwabciyarta kasar Ruwanda za ta karbi bakuncin gasar tseren keke ta duniya a kaka mai zuwa, wanda shi ne gasar tseren keke mafi girma da aka taba shiryawa a kasar. A karshen watan Janairun da ya gabata, Hukumar Kula da Tseren Kekuna ta Kasa da Kasa (UCI) ta ce ba a mika gasar tseren kekunan ta duniya zuwa wata kasa ba a lokacin da take mai da martani kan jita-jitar da ake yi game da yiwuwar shirin ko-ta-kwana.

Ruwanda | Paul Kagame | Shugaban KasaShugaban kasar Ruwanda Paul KagameHoto: Lim Yaohui/Newscom/Singapore Press Holdings/IMAGO Tennis | ATP | Jannik SinnerJannik Sinner na ci gaba da zama kan gaba a wasan tennis a duniyaHoto: Antonio Calanni/AP/picture alliance

Dan wasan tennis na kasar Brazil mai shekaru 18 a duniya João Fonseca da ke a matsayi na 99 a duniya, ya lashe gasar ATP 250 a birnin Buenos Aires a ranar Lahadin da ta gabata, inda ya samu kambunsa na farko bayan da ya doke dan wasan kasar Ajantina Francisco Cerundolo  da ci shida da hudu da bakwai da shida. Matashin na yankin kudancin Amurka, ya zama dan wasa na 10 mafi karancin shekaru da ya lashe gasar ATP tun daga shekarar 1990. Wannan nasarar ta sa Fonseca samun ci-gaban matsayi 31, inda yanzu ya kai matsayi na 68 a duniya. Amma dai har yanzu Jannik Sinner ne ke jan ragamar teburin tennis na duniya, yayin da Alexander Zverev ke biye masa baya shi kuma Carlos Alcaraz ke a matsayi na uku.

 


News Source:   dw.com