Wasanni: Gasar ci kofin zakarun Turai

A Bundesligar Jamus, Bayern Munich na ci gaba da zan zarenta a kan teburi duk da nasarar da mai rike da kambun Leverkusen ta samu, yayin da yaya karama Borusia Dorthmud ke nuna alamun farfadowa bayan zazzaga wa Union Berlin kwallaye 6,

A ingila kuwa da alama Liverpool ta kama hanyar zama zakarar Premier bayan doke Manchester City sannan Aresal ta yi rashin nasara a gida.

A Najeriya Jihar Katsina ta fito da shiri na tura matasa tara zuwa Turai domin samun horo da nufin kyankyashe sabbin zaratan 'yan wasan kwallon kafa.

An fidda jadawalin zagaye na gaba na gasar cin kofin zakarun nahiyar turai cikin sabon tsari inda aka tanadi wasanni masu sarkakiya tsakanin kungiyoyi 16 da suka yi nasarar darewa zuwa wannan mataki.

Kylian Mbape na - Paris Saint-Germain Hoto: Elyxandro Cegarra/NurPhoto/picture alliance

Wasanni da suka fi sarkakiya kuma ake sa ran komai na iya faruwa sun hadar da karawa 'yar gida tsakanin Real Madrid ta Kylian Mbappe da Atletico da Madrid wadanda a bana da kyar da jibin koshi suka tashi canjaras a wasannan mako na 23 na Laligar Spain. Hakazalika akwai karawa tsakanin Bayern Munich da Bayer Leverkusen wadda da kyar da jibin koshi yaya babba ta tsira a hannunta a wasan da suka buga a mako na 22 ta Bubdesligar kasar Jamus.

Wani babban wasa shine karawa tsakanin Liverpool wadda ta zama gagara badau da halin yanzu da Paris Saint Germain ta kasar Faransa wadda da kyar ta samu tikitin zuwa wannan mataki, sai karawa tsakanin Barcelona da Benfica wadanda suka yi kare jini biri jini a karshen watan Janairu duk da na nasarar da Blauo grana suka samu a karshen lokaci ci 5-4.

Sauran wasanni sun hadar da karawa tsakanin Arsenal da PSV Ndoven, Borussia Dortmund da Lille ta Faransa, Club Bruges da Aston Villa, sai kuma Feyenoord da Inter Milan

Za a buga zagayen farko da wadannan wasanni a ranakun 4 da 5 ga watan Maris zagaye na biyu ranakun 11 da 12 ga watan Maris din na 2025.

Jamal Musiala na Bayern MünichHoto: Marco Steinbrenner/DeFodi Images/picture alliance

A Bundesligar kasar Jamus Yaya babba Bayern Munich na ci gaba da cin karenta babu babbaka tare da yin kane-kane a kan teburin gasar da maki 50 cif bayan wasannin mako na 23. Tawagar ta Vincent Kompanie ta yi raga-raga da Frankfurt da ci 4-0 a filin wasa na Allianz Arena lamarin da ya bata damar yi wa Leverkusen zarra ta 8 duk da nasarar da tawagar ta Xavi Alonzo ta samu a kan 'yar baya ga dangi Holstein Kiel  da ci 2-0. Ita kuwa yaya karama Borissia Dortmud ta yi abin kai inda ta zazzaga wa Union Berlin kwallaye 6-0 cikin har da kwallaye uku da Girassi ya ci lamarin da ya ba ta damar tashi daga mataki na 11 domin kwace mataki na 10 a hannun Bremen wadda ta sha kashi a hannu Freiburg ci 5-0.

A sauran wasannin na Bundesliga kuwa Augsburg ta yi tattaki ta doke Mönchenglach a gaban walidai ci 3-0, Maiz ta casa St Pauli ci 2-1, Wolfsburg ta yi canjaras da Bochum ci 1-1, sai RB Leipzig da ke ci gaba da shiga rudani ta koma matsayi na 6 bayan ta fuskanci turjiya daga Heidenheim inda suka tashi ci 2-2, sannan ita ma kurar baya Hoffenheim da ke a mataki na 16 ta rike wuta a a gaban Stuttgart inda suka tashi canjaras ci 1-1.

Yan wasan Bayern München - Holstein KielHoto: Lukas Barth-Tuttas/AFP/Getty Images

Idan muka nufi Najeriya jihar Katsina ta aike da matasan 'yan wasan kwallon kafa kimanin guda tara domin samun horo a kasashen Turai da nufin kyankyashe sabbin 'yan wasa masu basira. Wannan ya biyo bayan ziyarar da wata Tawagar masu horarwa da farautar 'yan wasan kwallon Kafa da ta fito daga kasashen Faransa da Kanada ta kai jihar.

An yaye labulen kasar tseren kekuna ta Ruwanda a ranar Asabar da ta gabata duk kuwa da matakin da wasu kasashe suka dauka na kaurace wa wannan saboda zargin Kigali da hannu dumu-dumu kan rikicin da ake gwabzawa a gabashin Kwango.

A fagen wasan dambe kuwa dan damben Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango Martin Bakolé ya sha kashi a hannun takwaransa na kasar Newzeland Joseph Parker a yayin fafatawar da suka yi a rukunin masu nauyi a birnin Ryad na kasar Saudiyya a ranar Lahadi. Tun a turmi na biyu ne dai Joseph Parker ya kai Martin Bakolé kasa, to amma ana alakanta wannan lamarin da halin gajiya daga bangaren dan damben na Kwango domin cikin kurarren lokaci ya samu goron gayya domin maye gurbin dan damben kasar Burtaniya Daniel Dubois wanda ya kwanta rashin lafiya.

 

 

 


News Source:   dw.com