Wane Ne Zai Lashe Kyautar Ballon d’Or Ta Bana?

Wane Ne Zai Lashe Kyautar Ballon d’Or Ta Bana?

Jaridar kwallon kafa ta France Football ce ta kirkiri ba da wannan lambar yabo a shekarar 1956 don karrama dan kwallon da ya fi nuna bajinta a fagen tamaula.

Washington D.C. — 

A ranar Litinin 28 ga watan Oktoban bana, hankulan masoya kwallon kafa zai karkata zuwa birnin Paris na kasar Faransa domin kallon dan wasan da zai lashe kyautar Ballon Do’r – ta gwarzon kwallon kafar duniya.

Bikin ba da wannan kyauta a bana ya fita daban, kuma wasu da dama na kallonsa a matsayin wani sabon babi da za a bude a duniyar kwallon kafa duba da cewa a karon farko cikin shekaru 16 babu Lionel Messi da Cristiano Ronaldo a jerin gwarazan ‘yan wasan da aka tsamo don neman lashe wannan kyauta.

Sau takwas Messi ya lashe wannan kyauta yayin da Ronaldo ya lashe sau biyar.

Jaridar kwallon kafa ta France Football ce ta kirkiri ba da wannan lambar yabo a shekarar 1956 don karrama dan kwallon da ya fi nuna bajinta a fagen tamaula.

Ga jerin ‘yan wasan da akea tsamo don yin takara a wannan shekara ta 2024 a neman kyautar ta Ballon D’or kamar yadda shafin EUFA.COM ya wallafa.

Jude Bellingham (England, Real Madrid) Hakan Çalhanoğlu (Turkey, Inter) Dani Carvajal (Spain, Real Madrid) Rúben Dias (Portugal, Manchester City) Artem Dovbyk (Ukraine, Dnipro / Girona / Roma) Phil Foden (England, Manchester City) Alejandro Grimaldo (Spain, Bayer Leverkusen) Erling Haaland (Norway, Manchester City) Mats Hummels (Germany, Borussia Dortmund) Harry Kane (England, Bayern Munich) Toni Kroos (Germany, Real Madrid) Ademola Lookman (Nigeria, Atalanta) Emiliano Martínez (Argentina, Aston Villa) Lautaro Martínez (Argentina, Inter ) Kylian Mbappé (France, Paris Saint-Germain / Real Madrid) Martin Ødegaard (Norway, Arsenal) Dani Olmo (Spain, Leipzig / Barcelona) Cole Palmer (England, Manchester City / Chelsea) Declan Rice (England, Arsenal) Rodri (Spain, Manchester City) Antonio Rüdiger (Germany, Real Madrid) Bukayo Saka (England, Arsenal) William Saliba (France, Arsenal) Federico Valverde (Uruguay, Real Madrid) Vinícius Júnior (Brazil, Real Madrid) Vitinha (Portugal, Paris Saint-Germain) Nico Williams (Spain, Athletic Club) Florian Wirtz (Germany, Bayer Leverkusen) Granit Xhaka (Switzerland, Bayer Leverkusen) Lamine Yamal (Spain, Barcelona)


News Source:   VOA (voahausa.com)