Shahararren dan wasan kwallon kafa dan kasar Portugal Cristiano Ronaldo ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekaru 2+1 da tsohuwar gungiyarsa ta Manchester United.
Bayan yarjejeniyar da aka kulla da Juventus, dan wasan mai shekaru 36 zai sake saka rigar Manchester United bayan shekaru 12.
Ronaldo ya shaida cewa, "Na zaku na sake saka riga a gaban 'yan kallo tare da buga wasanni a Old Trafford."
A shekarar 2003 Ronaldo ya bar kungiyar Sporting Lizbon tare da komawa Manchester United inda ya lashe gasar Premier 3, League Cup 2, federation Cup 1, Comminity SHield 1, Gasar Zakarun Turai 1 Gasar FIFA ta Kasa da Kasa 1.