Tsohon mai rike da kambun zakaran damben boksin na duniya dan asalin Faransa ya mutu yana da shekaru 59, a cewar magajin garin mahaifarsa ta Calais a yau Juma’a.
Jacob ya karbe kambun damben boksin na WBC ajin masu nauyi a 1992, inda ya doke Daniel Zaragoza dan asalin Mexico a gaban magoya bayansa a birnin Calais.
“Mun wayi gari yau da mummunan labari. Thierry Jacob ya mutu a daren jiya” a cewar sanarwar da magajin garin birnin dake tashar ruwan arewacin Faransa, Natacha Bouchart ta wallafa a shafinta na Facebook.
Jacob ya zamo kwararren dan damben boksin a 1984, inda yayi ritaya bayan shekaru 10 da kafa tarihin 39-6, sannan ya rasa kambunsa na WBC a kokarinsa na farko na kareshi a hannun ba-Amurke Tracy Harris Patterson a birnin New York.
Daya daga cikin ‘ya’yansa, Romain Jacob, ya gaje shi a harkar damben boksin, inda ya samu kambun zakarun nahiyar Turai ajin marasa nauyi a 2014.