Sudan na samun ci-gaba a wasanni a yanayi na yakin basasa

Yakin da ya barke tsakanin sojin kasar da kuma mayakan RSF a Sudan a watan Afrilun 2023 ya haifar da koma baya a bangarori daban-daban ciki har da fannin wasanni, wanda a halin da ake ciki, ba lalle ne a mayar da hankali kan wasannin kwallon kafa ba, 'Yan wasa na cikin fargaba kan halin da ake ciki a Sudan, ko da yake hakan bai hana 'yan wasan karsashi domin samu nasara ba. Manyan kungiyiyon kwallon kafa na Al-Hilal da Al-Merrikh na buga wasanninsu a gasar Moritianiya a kakar wasannin bana. Sai dai  babu wata kungiya da za ta zama zakara ko da kuwa ta zo na daya. Yawancin 'yan wasan Sudanr na taka leda ne a wadannan manyan kungiyoyin inda horon da suke samu da kuma wasannin da suke yi ke taimaka musu matuka.

Karin bayani: 

Al-Hilal ta Omdurman na daga cikin kungiyoyin kwallon kafa da aka fi ji da su a SudanAl-Hilal ta Omdurman na daga cikin kungiyoyin kwallon kafa da aka fi ji da su a SudanHoto: Loveness Bernard/Sports/picture alliance/empics

A watan Oktoba ne Sudan ta kara da Ghana a gasar neman cancantar shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka inda suka yi kunnen doki a Accra. Sai dai, sun yi nasarar ci 2:0 a gida, lamarin da ya sanya Sudan kasancewa a matsayi na biyu a rukunin wasannin neman shiga gasar AFCON. A yanzu, tana neman maki biyu ne kacal a wasanninsu biyu na kasar domin samun tikitin shiga gasar a karo na hudu a cikin shekaru 49.  

Wannan nasara ta fara sanya farin ciki a zukatan 'yan Sudan da ma 'yan wasan kasar, duk da cewa har yanzu ana tsaka da yaki. Sai dai, wasu na ganin cewa idan har Sudan ta iya samun gurbin shiga wadannan manyan gasanin, tabbas duniya ba za ta taba mantawa da kasar ba, duk da cewar yaki ya daidaita ta

Abdelrahman Kuku, da ke taka wa Sudan leda ya bayyana cewar: "Wadannan nasarorin na taka mahimmiyar rawa a ayyyukanmu. Suna sa farin ciki da annashuwa ga mutanen da ba su da wani abun da za su yi murmushi a kai musamman idan suka tuna abun da ke faruwa a gida Sudan, inda mutane ke ci gaba da rasa rayukansu da matsugunnansu . Farin cikin da suke samu shi ne kadai lokacin da muke buga wasanni, saboda wannan lokacin ne suke ganin wani abun na ci gaba na faruwa a kasar."

Stephen Constantine ya horas da kungiyar kwallon kafar Sudan daga 2009 zuwa 2010.Stephen Constantine ya horas da kungiyar kwallon kafar Sudan daga 2009 zuwa 2010.Hoto: Zhong Zhenbin/dpa/HPIC/picture alliance

Aka fara samun kwarin gwiwar cewar Sudan za ta iya kai bantenta zuwa gasar cin kofin duniya ta shekarar 2026 da za ta gudana a kasashen Amirka ta Arewa, sai dai kuma Stephen Constantine, tsohon mai horas da 'yan wasan kasar Sudan, wanda yanzu ya koma horas da 'yan wasan kasar Pakistan na ganin cewar har yanzue da sauran runa a kaba. Constantine ya ce: "Idan Sudan ta samu tikitin shiga gasar cin kofin duniya, tasirin kasar zai karu musamman a bangaren kwallon kafa, wanda zai sa in yi la'akari da ita a tsakiyar jerin kasashen da ke taka leda a Afirka. Zai zama babbar dama. Zuwa gasar cin kofin duniya shi ne babban burin kowace kungiyar kwallon kafa a duniya amma ga Sudan da ke fama da wadannan tarin matsalolin. Sai dai kuma akwai sauran tafiya a yanzu."

Kwallon kafa na cikin zukatan kusan dukannin 'yan kasar Sudan da ke da yawan al'umma kusan miliyan 50. Duk da cewa kasar Sudan ba ta taba shiga gasar cin kofin duniya na kwallon kafa ba, amma mafarkinta na samun tikiti a wannan lokacin ya zama gaskiya. 


News Source:   dw.com