Ronaldo Ya Zubar Da Fenariti, An Cire Al Nassr A Gasar King’s Cup

Ronaldo Ya Zubar Da Fenariti, An Cire Al Nassr A Gasar King’s Cup

Ronaldo ya ci dukkan bugun fenariti 18 da ya yi a baya ga Al-Nassr, amma a wannan karon ya cilla ta saman raga.

Washington D.C. — 

Cristiano Ronaldo ya zubar da bugun daga kai sai mai tsaron raga ana gab da tashi a wasa.

Hakan na nufin Al-Nassr ta fita daga gasar King’s Cup ta Saudiyya bayan shan kashi da ci 1-0 a hannun Al-Taawoun.

Ronaldo, wanda ya taba lashe kyautar Ballon d’Or sau bai samu nasarar lashe babbar kofi ba tun bayan rattaba hannu da kulob din kimanin shekaru biyu da suka gabata.

A matakin zagaye na ‘yan 16 na gasar fitar da kwallo ta Saudi Arabiya, Al-Taawoun ta samu nasara bayan da Waleed Al-Ahmad ya ci kwallo da kai ana saura minti 20 a tashi daga wasan.

An zartar da hukunci a kan Al-Ahmad saboda laifi da ya tafka a minti na 95.

Ronaldo ya ci dukkan bugun fenariti 18 da ya yi a baya ga Al-Nassr, amma a wannan karon ya cilla ta saman raga.

News Source:   VOA (voahausa.com)