Kungiyar kwallon kafa ta Porto ta sanar da sallamar Vitor Bruno a jiya Litinin, abinda ya kawo adadin kulub-kulub din kasar Portugal 3 da suka sallami masu horas dasu a wannan kaka.
Daraktan makarantar horas da wasan kwallon kafa ta Porto Jose Tavares zai karbe ragamar horas da kungiyar a mataki na wucin gadi, kamar yadda kulub din ya bayyana.
Porto ta subuto zuwa mataki na 3 a saman teburi, inda take a bayan Sporting da maki 4. Benfica ta matsa zuwa mataki na 2 a karshen makon daya gabata.
Benfica ta raba gari da kociyanta dan asalin Jamus Roger Schmidt a karshen watan Agusta, yayin da Sporting ta sallami mai horaswar daya gaji Ruben Amorim Joao Pereira fiye da wata guda bayan da Amorim din ya koma Manchester United.