A yau Juma’a za a bude gasar wasannin Olympics ta shekarar 2024 a hukumance, inda 'yan wasa sama da 10,000 zasu hallara a birnin Paris, suna fatan lashe lambar yabon zinariya, azurfa ko tagulla.
WASHINGTON D.C. —Sai dai daga cikin su har da mata da yawa daga kasashen Afirka, wadanda da yawansu su ka jure wa kalubale da yawa don zuwa Paris.
A karon farko a tarihi, kwamitin wasannin Olympic na duniya, da ake kira IOC, ya bayyana cewa an samu cikakken daidaiton jinsi a fagen wasan gasar Olympics ta bana.
Mata 'yan wasa, wadanda a baya suka kasance kusan kashi 2 cikin 100 na masu fafatawa a gasar Olympics, a yanzu kusan yawan su daya da maza.
Mata ne kashi 48 cikin 100 na ‘yan wasan gasar Olympics da aka yi a Tokyo shekaru uku da suka wuce, wanda aka jinkirta da shekara daya saboda annobar COVID-19.
Matan Afirka da dama na daga cikin wadanda za su fafata a gasar.
Esti Olivier ‘yar wasan tseren kwale-kwale ce, daya daga cikin masu wakiltar Afirka ta Kudu.
A karon farko za ta fafata a gasar Olympics bayan da ta rasa damar zuwa wasannin Tokyo saboda rashin lafiya da ta fuskanta.