Paris 2024: 'Yar Algeriya Kaylia Nemour Ta Lashe Kyautar Zinare

Paris 2024: 'Yar Algeriya Kaylia Nemour Ta Lashe Kyautar Zinare

Nemour ta samu damar fafatawa a karkashin tutar Algeriya ne bayan da kungiyarta ta samu sabani da hukumar wasannin tasalle-tsallen Faransa ne.

WASHINGTON D.C. — 

Kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito cewa ‘yar kasar Algeriya Kaylia Nemour ta lashe kyautar zinare a wasan tsalle-tsalle a gasar wasannin Olympics, kyautar zinare ta farko da kasar Algeriya ta samu a wasannin tsalle-tsalle bayan da ta nuna bajintarta sannan ta doke ‘yar kasar China Qiu Qiyuan.

Ita kuma Sunisa Lee ta lashe kyautarta ta 3 a wasannin na Paris wanda ya tasanma kyaututtuka 6 da ta samu a wasannin Olympics, bayan da ta samu kyautar tagulla kamar yadda ta samu a wasannin Olympics din da aka yi a birnin Tokyo shekaru 3 da su ka gabata.

Nemour ‘yar Faransa ce sannan har yanzu tana samun horo a kasar ta Faransa, sai dai kuma ta koma yiwa kasarta ta asali Algeriya wasa bayan wani rashin jituwa da ta shiga tsakaninta da hukumar wasannin tsalle-tsallen kasar Faransa da kungiyar da Nemour take yiwa wasa Ayoine Beamount, wanda ya yi sanadiyyar ‘yar wasan tsalle-tsallen ta rungumi kasar mahaifinta na asali Algeriya.

‘Yar wasannin tsalle-tsallen mai shekaru 17 ta kware sosai a fannin tsalle-tsallen da ake yin shi tsakanin turaku.

Yayin da Nemour take wakiltar wata kasa, ta rataya tutar kasar Algeriya a kafadarta bayan da ta yi nasara, tamkar dai a gida take.

Ita kuma Lee ta kwashe tsawon watanni 15 tana fama da cutar koda wanda ya janyo mata cikas wajen samun damar shiryawa da kyau. Don bata mai da hankali sosai a kan wasanni na Olympics ba sai zuwa watan Disamba.

Bayan da ta baiwa tawagar ‘yan wasar tsalle-tsalle mata ‘yan Amurka da Simone Biles ta jagoranta har su ka samu kyautar zinare, Lee ta lashe kyautar tagula, wuni biyu bayan nan tare da taimakon Biles da Rebeca Andrade ‘yar Brazil.

AP


News Source:   VOA (voahausa.com)