Paris 2024: Tawagar Kwallo Kwando Ta Matan Najeriya Ta Isa Kwata Fainal

Paris 2024: Tawagar Kwallo Kwando Ta Matan Najeriya Ta Isa Kwata Fainal

‘Yar wasan kwallon Kwandon mata ta Najeriya Ezinne Kalu ta yi nasarar samar wa kungiyar ta maki 21 kana Najeriya ta kafa tarihi ta bangaren maza da mata a gasar Olympics, inda ta zama kasar Afrika ta farko da ta isa wasan kwata fainal na kwallon kwando a wasannin Olympics.

'Yan wasan na Najeriya sun lallasa takwarorin su na kasar Canada ne da ci 79 da 70 a ranar Lahadi.

Wannan nasara ta 2-1 da ‘yan Najeriya suka samu na zuwa ne a lokacin Najeriya ta ke da nasara daya a wasannin Athens na 2004, amma yanzu zata dauki lokacin mai yawa da bata taba yi ba a gasar Olympics. Najeriya zata kara ne da Amurka, wadda ke neman daukar lambar zinari a karo na 8 jere.

Babu wani abin damuwa da abokin karawa na gaba bayan nasara kan Canada.

'Yan wasan Najeriya suke murna bayan sun lallasa 'Yan Canada da ci 79-70 'Yan wasan Najeriya suke murna bayan sun lallasa 'Yan Canada da ci 79-70

Kalu da abokan wasanta sun je tsakiyar filin wasan suna nuna farin ciki, inda mataimakiyar mai horaswa ta yi amfani da wayarta ta nadi murnar tasu. ’Yan Najeriya sun tsaya suka daga wa ’yan kasar Canada hannu na sallama, sannan suka ci gaba da murna a tsakiyar filin wasan.

Canada, da ke matsayin na 5 a duniya, ta fice daga wasan ba tare da samun nasara ba a wasanni uku da ta yi, a karshe kungiyar kwallon Kwando ta mata da ke matsayin na 12 a duniya ta yi waje da ita.

'Yar wasan Kwallon Kwandon Canada 'Yar wasan Kwallon Kwandon Canada

Australia ta doke Faransa da ci 79-72 a wasan karshe na rukunin da suka fafata a daren Lahadi. Nasara lashe wasanni 2-1 da kungiyar kwallon Kwando ta matan Australia mai ikiya “The Opals” ta yi, ya kai ta ga samu matsayi na 8 kuma na kwata fainal, inda ta kauce wa yin waje a gaban taron mutane 27,193 da kungiyar kwallon Kwando ta duniya FIBA ta ce sun kafa tarihin halartar gasar kwallon kwando ta mata a Turai.

‘Yan kasar Australia za su fafata wasan kwata fainal na farko ne da kasar Serbia a ranar Laraba. Kasar Spain kuma zata raba rana da Belgium kana Faransa zata kara da Jamusa sannan Amurka da Najeriya za su ba hammata iska.

Yayin da Najeriya da Canada ke fafatawa Yayin da Najeriya da Canada ke fafatawa

Najeriya ta gaza samun gurbin shiga gasar a Rio de Janeiro a shekarar 2016, kuma bata yi nasarar lashe wasa ba a gasar ta Tokyo. An hana wannan tawagar mata shiga kwale-kwalen Najeriya a lokacin bukin bude gasar a ranar 26 ga watan Yuli, kuma yanzu za ta yi wasan Laraba a dandalin Bercy Arena da ke gabar kogin Seine.


News Source:   VOA (voahausa.com)