Neymar Na Tattaunawa Domin Barin Al-Hilal

Neymar Na Tattaunawa Domin Barin Al-Hilal

Yarejeniyar Neymar da Al-Hilal na nan har zuwa watan Yuni mai zuwa.

washington dc — 

Tauraron kwallon kafar Brazil Neymar na tattauawa akan barin kungiyar Al-Hilal ta kasar Saudiyya sai dai bukatunsa na kudi na hana yarjejeniyar rushewa, kamar yadda wata majiya a kungiyar ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP a yau Laraba.

Majiyar, wacce ta nemi a sakaya sunanta tace, “Neymar na tattaunawa akan raba gari da kungiyar Al-Hilal saidai tsananin bukatar kudinsa ta zama babbar matsala.”

Yarejeniyar Neymar da Al-Hilal na nan har zuwa watan Yuni mai zuwa.

Rahotanni a Brazil na cewar kungiyar Santos na tattaunawa da shi domin komawa mahaifarsa amma Al-Hilal zata fi kaunar yin musaya yayin da Neymar ke bukatar yarjejeniyar aro.


News Source:   VOA (voahausa.com)