Kungiyar ta Najeriya, wacce ta lashe kofin Afirka sau uku, tana matsayi na 39 a duniya a baya.
Washington D.C. —Super Eagles ta Najeriya ta haura matsayi uku a sabon jadawalin kungiyoyin kwallon kafa na maza da Hukumar Kwallon ƘKafa ta Duniya (FIFA) ta fitar.
FIFA ta fitar da sabon jadawalin kungiyoyin maza a shafinta na yanar gizo a ranar Alhamis.
Kungiyar ta Najeriya, wacce ta lashe kofin Afrika sau uku, tana matsayi na 39 a duniya a baya.
Super Eagles ta kuma tashi daga matsayi na shida zuwa na hudu a iya kwallo a nahiyar Afirka.
Super Eagles ta doke Libya da ci 1-0 a wasan neman cancantar shiga gasar cin Kofin Afirka na 2025, wanda shi ne kadai wasan da suka yi a watan Oktoba.
An dage wasa na biyu da bangarorin biyu za su kara a Libya, baayn d Super Eagles ta janye daga wasan saboda korafin an yasar da su a filin jirgi, zargin da hukumomin Libya suka musanta.