Sanarwar ta kara da cewa Ruud van Nistelrooy zai maye gurbin Ten Hag a matsayin kocin rikon kwarya tare da sauran ma'aikatan da suka yi aiki tare da tsohon kocin.
washington dc —Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta kori kocinta Erik ten Hag sakamakon rashin nuna bajinta da kungiyar ta yi a kakar wasa ta bana, in ji kungiyar ta Premier a ranar Litinin.
United ta koma mataki na 14 a teburin gasar bayan ta sha kashi karo na hudu a wasanni tara a West Ham ranar Lahadi, inda wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta ce: "Erik ten Hag ya bar mukaminsa na kocin Manchester United na maza."
Sanarwar ta kara da cewa Ruud van Nistelrooy zai maye gurbin Ten Hag a matsayin kocin rikon kwarya tare da sauran ma'aikatan da suka yi aiki tare da tsohon kocin.