Labarin Wasnni: Mu leka duniyar wasanni

An shiga zagayen karshe na neman cancantar halartar gasar cin kofin nahiyar Afirka masu buga wasa a cikin gida wato CHAN,wadda za a fafata a badi. Kasashen da za su kara da juna a zagayen na karshe sun hada da Liberia da Senegal, sai kuma Mauritania da Mali sai takwayen kasashe wato Guinea da Guinea-Bissau. Jamhuriyar Nijar za ta fafata da Togo, kana Cote d'Ivoire da Burkina Faso sai kuma a kece raini tsakanin Ghana da Najeriya. Kasashen Kenya da Yuganda da kuma Tanzaniya ne za su karbi bakuncin gasar, daga ranar daya ga watan Fabarairun sabuwar shekara ta 2025 zuwa karshensa.

Gianni Infantino | FIFAShugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA Gianni InfantinoHoto: Brennan Asplen/Getty Images

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA ta fitar da jadawalin gasar cin kofin zakarun kungiyoyin duniya wato FIFA Club World Cup na badi, wanda a karon farko aka fadada shi zuwa kungiyoyi 32 maimakon shida ko takwas da aka saba gani a baya. An raba kungiyoyin ne zuwa rukunoni takwas.

Tseren Motoci | Lewis HamiltonShahararren dan wasan tseren motoci na duniya Lewis HamiltonHoto: Darko Bandic/AP/picture alliance

A gasar tseren mota ta Formula One direban marsandi Lewis Hamilton ya nuna farin cikinsa bayan da ya kwashe tsawon shekaru 12 yana tuka musu mota, wanda ya lashe gasar har sau bakwsai a tarihi. A yanzu Hamilton zai koma kamfanin Ferrari, a sabuwar shekara mai kamawa ta 2025.

Australian Open | TennisGasar Tennis ta Australian OpenHoto: Morgan Hancock/Getty Images

Fitattun 'yan wasan kwallon Tenis na duniya, sun bayyana aniyarsu ta shiga gasar Australian Open ta watan Janairun badi. Wadanda suka sanar da fafatawarsu a gasar sun hada da Nick Kyrgios da Jack Draper da Cameron Norrie da Katie Boulter da Emma Raducanu da  Sonay Kartal da kuma Jodie Burrage.


News Source:   dw.com