Labarin Wasanni: Neman gurbi a gasar AFCON

Ita kuwa Najeriya ta bai wa marada kunya, inda ta mamaye Jamhuriyar Benin da ci uku da nema a ranar Asabar a filin wasa na Godswill Akpabio. Ademola Lookman ne ya fara nuna bajinta, sannan Victor Osimhen ya ci kwallo na biyu kafin Lookman ya zura kwallo na uku da hakan ya bai wa Super Eagles kwarin gwiwa kafin hduwar ta da Ruwanda. Ita kuwa Kamaru ta doke Namibiya da ci daya da nema, bayan da Vincent Aboubakar ya ci kwallo a Garoua a minti na 65. 'Yan wasan Indomitable Lions sun fuskanci turjiya daga takwarorinsu na Namibiya, lamarin da ka iya sa su tararradi gabanin karawarsu da Zimbabuwe. Ita ma Muritaniya ta samu nasara a kan Botswana da ci daya mai ban haushi, kana Tunisiya ta taka rawar gani inda ta doke Gambiya da ci byiu da daya. Wannan dai ita ce nasara ta biyu da Tunisiya ta yi a wasanni biyu, bayan lallasa Madagaska da ta yi da ci daya da nema. Kasashe biyu na farko na kowane rukuni ne kawai za su haye zuwa gasar AFCON ban da Maroko da ke daukar bakunci, lamarin da ke kara muhimmanci neman nasara domin cancantar shiga gasar a 2025.

Senegal | Kwallon Kafa | AFCONTawagar kwallon kafa ta SenegalHoto: Getty Images/AFP/A. Ouoba

An shiga mataki na biyu a wasannin neman tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka, wadda za ta gudana a Maroko a shekarar da ke tafe ta 2025. Kasashen da aka fi ji da su da suka hada da Najeriya da Kamaru da Côte d' Ivoire sun yi kokarin karfafa matsayinsu a wasansu na farko, yayin da sauran kasashe masu karfi kamar Ghana da Senegal ke neman yin gyara bayan da suka kasa kai labari a wasan farko. Senegal da ta lashe gasar a 2021 ta tsinci kanta a cikin wani yanayi na ba-zata, bayan kunnen doki daya da daya da ta yi a gida da Burkina Faso. Amma domin neman ramuwar gayya, Lions na Teranga ta Senegal, na shirin kalubalantar Burundin da ta yi nasara a kan Malawi da ci uku da biyu. Ita kuwa Ghana da ta lashe AFCON sau hudu tana fama da zullumi bayan da Angola da doke ta da ci daya da nema, lamarin da ke dagula mata lissafi a gabanin karawarta da Jamhuriyar Nijar.

Kamaru | Kwallon Kafa | MataTawagar 'yan wasan kwallon kafa mata ta KamaruHoto: Reuters/B. Szabo

'Yan matan Kamaru sun cancanci zuwa zagaye na biyu na gasar neman cin kofin kwallon kafar mata ta 'yan kasa da shekaru 20 da ke gudana a Colombia, bayan da suka doke Austaralia  da ci biyu da nema. Duk da cewa wannan shi ne karon farko da suka shiga gasar cin kofin duniya ta mata 'yan kasa da shekaru 20 amma Indomitable Lionness sun samu maki hudu a wasanni uku, inda suka zama na uku a rukuninsu. Su ma 'yan matan Najeriya sun haye mataki na gaba, inda za su yi wasansu na gaba da Japan a ranar Jumma'a yayin da aka yi waje da 'yan kasa da shekaru 20 na Ghana. A nasu bangaren, 'yan matan Faransa sun samu damar hayewa bayan da suka yi wa takwarorinsu na Fuji ruwan kwallaye 11 da nema. Su ma 'yan Mexico sun samu damar hayewa duk da cewa 'yan Colombia sun doke su da ci daya mai ban haushi a wasansu na karshe, saboda sun kasance a matsayi na biyu na rukuninsu. Kazalika 'yan matan Kanada sun bi sawun takwarorinsu na Brazil wajen samun tikitin zuwa zagaye na gaba, duk da kashi da suka sha a hannun 'yan matan Brazil ci biyu da nema. Sauran kasashen da suka haye sun hada da Jamus da Ajentina da Holland da Koriya ta Kudu da Amurka da Spaniya. A nahiyar Turai kuwa, kasashe dabam-dabam sun gudanar da wasannin "Nations League" da UEFA ke shiryawa tun shekaru shidan da suka gabata, wanda kuma ya bambanta da gasar zakarun Turai. Portugal ta zama kasa ta farko da ta lashe kofin, yayin da Faransa ta zama biyu ita kuma Spaniya ke rike da kofin a yanzu. Spaniyan ce dai ta fi zazzaga kwallaye a wasannin rukuni, inda ta lallasa Switzerlanda da ci hudu daya yayin da Sweden ta gasawa Estonia aya a hannu da ci uku da nema. Ita kuwa Potugal ta samu nasara a kan Scotland da ci biyu da daya, yayin da Slovakia ta doke Azarbaijan da ci biyu da daya. Sai dai wasu 'yan wasan kwallon kafa da kuma masu horaswa na kasashen Turai, sun koka game da yawan gasanni. 'Yan wasan irin su Kevin De Bruyne sun  zargi hukumomin kwallon kafa na duniya da yin illa ga lafiyar 'yan wasa, domin samun karin kudin shiga ta hanyar kara wasanni kamar "Nations League". A fagen tennis, bayan da Aryna Sabalenka ta lashe wasan rukunin mata na gasar US Open a gaban Jessica Peluga a ranar Asabar da ta gabata, shi kuwa Yannik Sinner dan Italiya ne ya lashe rukunin maza a ranar Lahadia sakamakon doke Ba'amurke Taylor Fritz a ci shida da uku da shida da hudu da bakwai da biyar. Wannan shi ne karo na biyu da yake lashe gasar Grand Slam a bana, bayan gasar Australian Open. Wannan sabuwr bajintar ta Sinner ta zo ne makonni uku bayan cece-kuce sakamakon gwajin da ya nuna cewar yana shan maganin kara kuzari, ko da yake wata hukuma mai zaman kanta ta wanke shi daga wannan zargi. Chaina ta zo na daya a yawan lambobi a gasar paralympics ta masu bukata ta musamman da aka kammala a birnin Paris na kasar Faransa, bayan shafe makonni biyu ana gudanar da wasanni dabam-dabam. Nahiyar Afirka ta taka rawar gani, inda 'yan wasanta suka samu lambobi 63. Maroko ta kasance a kan gaba wajen samun lambobi 15, amma kamar yadda ya wakana a birnin Tokyo a 2021 Chaina ce ta sake yin fice da lambobin zinare 94 da a takaice ya ninka na Birtaniya da ta zo ta biyu a gaban Amurka. Wannan gasa ta paralympics ta haska wasu sababbin taurari daga kasar Chainan, ciki har da 'yar lninkaya Yuyan Jiang mai shekara 19 da ta tashi da lambobin zinare bakwai kuma ta zama 'yar wasa mafi nasara a birnin Paris. Dama dai Chaina ta kasance tawaga mafi girma da 'yan wasa 284, wadanda suka fafata a fannonin wasani 20 daga cikin 22 da ake da su. 'Yan kasar Chaina sun samu lambobin zinare 22 a wasan ninkaya, 21 a wasannin guje-guje da tsalle-tsalle da kuma 11 a wasan tennis.

Paralympics | Paris 2024 | Linkaya | ChainaWasan linkaya, na daga cikin wasannin da Chaina ta yi zarra a gasar Paralympics 2024Hoto: Emilio Morenatti/AP Photo/picture allianceUS Open 2024 | Tennis | Aryna Sabalenka GWarzuwar gasar tennis ta US Open Aryna Sabalenka Hoto: Fatih Aktas/Andalou/picture allianceTurai l Kwallon Kafa l Nations League | PortugalPortugal na daga cikin kungiyoyin da suka kai bantensu a gasar Nations LeagueHoto: Patricia de Melo Moreira/AFP

 


News Source:   dw.com