Labarin Wasanni: Muleka duniyar wasanni

A karshen mako Borussia Dortmund ta sha kashi da ci biyu da daya a gida, yayin da Stuttgart ta yi tattaki zuwa birnin na Dortmund. Haka ma Hoffenheim ta wkashi nata kashin a hannun Unioin Berlin da ci hudu da nema a gida. Freiburg ta karbi bakuncin Heidenheim, ta kuma lalalsa ta da ci daya mai ban haushi. An tashi wasa canjaras babu ci tsakanin Wolfsburg da Leverkusen, haka abin yake a wasan da aka fafata tsakanin Mainz da Augsburg kana aka tashi wasa kunnen doki daya da daya a karawa tsakanin Borussia Monchengladbach da Eintracht.

Visit Rwanda | Bundesliga 2024 | Bayern | JamusAlakar Bayern Munich da RuwandaHoto: Bernd Feil/M.i.S./IMAGO

Wata yarjejeniya tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich da ke Jamus da kuma kasar Ruwanda, ta kasance wadda yanzu ake saka mata ido. Kasar ta Ruwanda ta shiga idon duniya, saboda irin zargin da ake mata na tayar da rikici a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. Ruwanda dai, na da yarjejeniya tsakanin Hukumar Yawon Bude Ido ta kasar da kuma kungiyoyin kwallon kafa na kasashen Turai da suka hada da Bayern Munich da ke Jamus da Paris Saint-Germain ta Faransa da kuma Arsenal ta Ingila. Ana daukar Shugaba Paul Kagame na Ruwanda wanda ya shafe shekaru 25 kan madafun iko, a matsayin kanwa uwar gami game da rikicin na gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.

IOC | Thomas Bach | Olympics Shugaban Hukumar Kula da Wasannin Olympics mai barin gado Thomas BachHoto: FABRICE COFFRINI/AFP/Getty Images

'Yan takarar da ke neman maye gurbin Thomas Bach a matsayin shugaban Hukumar Kula da Wasannin Guje-guje da Tsalle-tsalle ta Duniya wato Olympics, sun gabatar da matakin da za su dauka da abin da suke gani game da 'yan wasan da suka sauya halitta daga maza zuwa mata ko mata zuwa maza. Haka ya biyo bayan wata doka da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya gabatar, wadda ta hana duk wanda ya sauya halitta shiga gasar. Biyu daga cikin 'yan takara bakwai ba su ce komai game da batun ba sauran biyar din kuma na da ra'ayoyi mabambanta, inda wasu suke gani ya kasance daga wasu zuwa wasa kan duk wani matakin da ya dace a dauka. Wannan batu na 'yan wasan da suka sauya halitta, abu ne da zai ci gaba da janyo muhawara da takun saka na wani lokaci.

 


News Source:   dw.com