Kwalambiya: 'Yan matan Najeriya na bajinta

Wannan nasarar da 'yan matan na kasashen biyu suka samu, ta kara musu karfin fada a ji a nahiyarsu. Najeriyar da Maroko da Ghana da kuma Kamaru ne, suka samu damar halartar gasar a wannan karon. Kafin tawagar 'yan matan Najeriyar ta samu kanta a wannan matsayi, sai da ta fafata da takwarorinta na Venezuela da Jamus da kuma Koriya ta Kudu. A wasansu da Koriya ta Kudu ta samu nasara da ci daya da nema yayin da lallasa Venezuela da ci hudu da nema. A wasan da ta fafata da da Jamus kuwa, ta sha kashi ne da ci uku da daya. Sai dai duk da wannan kalubale da ta fuskanta a zagaye na farko na wasan kafin tsallakewa zuwa rukunin na 'yan 16, masu sha'awar wasanni kamar Khadija Ibrahim na ganin akwai sauran fata na kai wa mataki na gaba ganin irin jajircewar da suka nuna har ma asuka karkare da maki shida kamar takwarorinsu na Jamus da ke saman tebur a rukuninsu.

Mata na fuskantar kalubalen wasan kwallon kafa a Najeiriya

To view this video please enable JavaScript, and consider upgrading to a web browser that supports HTML5 video

Video Player is loading.PlaySkip BackwardSkip ForwardMuteCurrent Time 0:00/Duration 0:00Loaded: 0%Stream Type LIVESeek to live, currently behind liveLIVERemaining Time -0:00 1xPlayback RateChaptersChaptersDescriptionsdescriptions off, selectedSubtitlessubtitles settings, opens subtitles settings dialogsubtitles off, selectedAudio TrackQualityPicture-in-PictureFullscreen

This is a modal window.

Beginning of dialog window. Escape will cancel and close the window.

TextColorWhiteBlackRedGreenBlueYellowMagentaCyanOpacityOpaqueSemi-TransparentText BackgroundColorBlackWhiteRedGreenBlueYellowMagentaCyanOpacityOpaqueSemi-TransparentTransparentCaption Area BackgroundColorBlackWhiteRedGreenBlueYellowMagentaCyanOpacityTransparentSemi-TransparentOpaqueFont Size50%75%100%125%150%175%200%300%400%Text Edge StyleNoneRaisedDepressedUniformDrop shadowFont FamilyProportional Sans-SerifMonospace Sans-SerifProportional SerifMonospace SerifCasualScriptSmall CapsResetDoneClose Modal Dialog

End of dialog window.

02:15

Da take karin haske kan yadda gasar ta Kwalambiya ke gudana, jami'ar yada labarai ta kungiyar 'yan wasan kwallon kafa ta Najeriya ta mata 'yan kasa da shekaru 20 a Hukumar Kula da Wasannin Kwallon Kafa ta Najeriya Salma Yusuf da ta kasance mamba a kungiyar Marubuta Wasanni ta Najeriya reshen jihar Kano kana ma'aikaciya mai sharhi kan al'amuran wasanni a gidan radiyon Freedom da ke Kanon da a yanzu haka ke tare da tawagar ta Nigeria Falconets a Kwalambiyan ta ce, daga irin rawar da 'yan wasan ke taka waa yanzu akwai kyakkyawan fata cewa za su tsallaka zuwa zagaye na gaba a fafatawar da za su yi a Jumma'ar da ke tafe tare da Japan har ma su iya lashe kofin domin da ma fatansu ke nan.

'Yar wasan kwallon kwandon Najeriya

To view this video please enable JavaScript, and consider upgrading to a web browser that supports HTML5 video

Video Player is loading.PlaySkip BackwardSkip ForwardMuteCurrent Time 0:00/Duration 0:00Loaded: 0%Stream Type LIVESeek to live, currently behind liveLIVERemaining Time -0:00 1xPlayback RateChaptersChaptersDescriptionsdescriptions off, selectedSubtitlessubtitles settings, opens subtitles settings dialogsubtitles off, selectedAudio TrackQualityPicture-in-PictureFullscreen

This is a modal window.

Beginning of dialog window. Escape will cancel and close the window.

TextColorWhiteBlackRedGreenBlueYellowMagentaCyanOpacityOpaqueSemi-TransparentText BackgroundColorBlackWhiteRedGreenBlueYellowMagentaCyanOpacityOpaqueSemi-TransparentTransparentCaption Area BackgroundColorBlackWhiteRedGreenBlueYellowMagentaCyanOpacityTransparentSemi-TransparentOpaqueFont Size50%75%100%125%150%175%200%300%400%Text Edge StyleNoneRaisedDepressedUniformDrop shadowFont FamilyProportional Sans-SerifMonospace Sans-SerifProportional SerifMonospace SerifCasualScriptSmall CapsResetDoneClose Modal Dialog

End of dialog window.

02:21

A Najeriya, 'yan wasa dabam-dabam kan yi korafi dangane da matsalar rashin biyansu kudi da alawus dinsu. Shin ko Falconets na Najeriya na da wannan korafi? Salma Yusuf ta nunar da cewa kawo yanzu babu wannan korafin, kuma tun ma da ake wasannin sa da zumunta 'yan matan ke cin moriyar alawus dinsu da ma ihsani daga mahukunta. Kasashen da suka rage a cikin gasar a yanzu dai, sun hadar da Faransa da Mexico da mai masaukin baki Kwalambiya da Jamus da Kanda da Brazil da Ajentina da Holland da Koriya ta Kudu da Amurka da Spaniya da Kamaru da kuma Japan da za ta fafata a Jumma'ar da ke tafe tare da Najeriya. Kungiyoyi 24 ne suka shiga gasar, kafin ayi waje da takwas kana 16 su yi saura wadanda suma za a tankade a rairaye su zuwa takwas a nan gaba.

News Source:   dw.com