Luis Diaz ya kasa danne farin cikinsa da hawaye a lokacin da yake magana kan James Rodriguez, wanda ya jagoranci tawagar Colombia zuwa wasan karshe a gasar cin kofin Copa America da za su fafata da Argentina a ranar Lahadi.
Dan wasan Liverpool Diaz ya ce “daga lokacin da ya isa tawagar kasar, na sanar da shi cewa shi ne gwanina.” Na girma ina kallonsa.
Irin wannan kauna ta dan wasan tsakiyar, wanda ya cika shekaru 33 a ranar Juma’a, ke jan hankali a sansani ‘yan wasan Colombia.
Diaz mai shekaru 27 yana matashi ne lokacin da James ya nuna bajinta a gasar cin Kofin Duniya ta 2014 a Brazil, inda ya lashe takalmin zinare a matsayin wanda ya fi zura kwallaye a gasar, sannan ya bar kungiyar Monaco ya koma zuwa Real Madrid.
Amma ga wannan gasar cin kofin Copa America ta bana, ana sa ran James zai taka rawa kadan.
Ya isa Amurka ne bayan rashin taka rawa a wannan kakar wasa ta bana a kulab din Sao Paulo na Brazil, inda yake kan hanyarsa ta barin kungiyar bayan irin rawar da ya taka.
Burin Colombia na lashe kofin Copa na biyu an daura shi a kan Diaz, tare da Jefferson Lerma da Daniel Munoz, wasu ‘yan wasa biyu da ke taka rawa sosai a Ingila.