Hukumomin Faransa Sun Dakile Kulle-kullen Tada Hargitsi A Gasar Olympics Ta Paris

Hukumomin Faransa Sun Dakile Kulle-kullen Tada Hargitsi A Gasar Olympics Ta Paris

Za’a fara Wasannin a hukumance tare da bikin budewa mai kayatarwa da kwararan matakan tsaro a River Seine a ranar Juma’a.

WASHINGTON D.C. — 

Hukumomin kasar Faransa sun dakile wasu kulle-kulle da za su kawo cikas ga wasannin motsa jiki na Olympics 2024, kamar yadda jami’ai su ka bayyana a ranar Laraba, kwanaki biyu gabanin bikin bude Wasannin Bazara a birnin Paris.

Kasar Faransa ta kasance cikin shirin ko-ta-kwana a cikin ‘yan makonnin da su ka wuce, yayin da shirye-shiryen karbar bakuncin gasar Olympics ta kai matakin karshe.

Za’a fara Wasannin a hukumance tare da bikin bude wa mai kayatarwa da kwararan matakan tsaro a River Seine a ranar Juma’a.

Masu gabatar da kara a birnin Paris sun fada a ranar Laraba cewa, sun kama wani mutum dan shekaru 40 haifaffan kasar Rasha a ranar Talata, a gidansa da ke birnin Paris bisa zarginsa da shirin tayar da fitina a Wasannin Olympics.

An tuhume shi da laifin “gudanar da aikin leken asiri bisa umarnin wata kasar waje” da nufin tada tarzoma a Faransa, laifukan da hukuncisu shi ne daurin shekaru 30 a Faransa, a cewar wata sanarwa daga ofishin mai shigar da kara na Paris.

A wani bincike da aka gudanar a gidan wanda ake zargi a Paris, jami’an ‘yan sanda sun gano wasu abubuwa da cewa “sun haifar da fargaba ta yiwuwar shirya abubuwa da ka iya haddasa tada zaune tsaye a gasar Olympics,” in ji masu gabatar da kara.

Masu shirya wasannin dai na fuskantar manyan kalubalen tsaro da suka hada da damuwa na hare-hare ta intanet, a daidai lokacin da kasashen duniya ke fama da tashe-tashen hankula saboda yakin da Rasha ke yi a Ukraine da kuma rikicin Isira’ila da Hamasa a Gaza.


News Source:   VOA (voahausa.com)