Tadej Pogacar ya zama dan tseren keke na farko da ya lashe tagwayen kambu na Giro d'Italia/Tour de France double, tun bayan shekara ta 1998. Dan kasar Soleveniya da ya lashe kambunsa na uku a Lahadin karshen mako, ya samu nasara a matakin karshe na nasarorinsa shida da ya samu a gasar. Pogacar ya lallasa takwaransa dan kasar Denmark da ke rike da kambun Jonas Vingegaard da kuma dan kasar Beljiyam Remco Evenepoel da suka zo na biyu da na uku a matakin karshe na gasar da tazarar mintuna shida da dakika 17.
Rafa Nadal dan kwallon Tennis na duniyaHoto: Jean-Francois Badias/AP/picture allianceShahararren dan wasan Tennis din nan Rafael Nadal ya samu koma-baya, a shirye-shiryensa na halartar gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle wato Olympics ta 2024 da birnin Paris fadar gwamnatin Faransa ke daukar nauyi. Nadal ya sha kashi a Lahadin karshen mako yayin wasan karshe na gasar Swedish Open, a hannun takwaransa Nuno Borges na Portugal da ci shida da uku da shida da biyu. Dan kasar Spaniyan mai shekaru 38 a duniya da ya fafata a wasansa na farko na neman lashe kambu tun bayan na French Open da ya lashe a shekara ta 2022, sai dai kuma hakarsa ba ta cimma ruwa ba.
Birnin Paris na shirin karbar bakuncin 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na duniyaHoto: Tasos Katopodis/Getty ImagesYanzu haka kwanaki hudu suka rage a fara wasannin na guje-guje da tsalle-tsalle na duniya, a birnin na Paris fadar gwamnatin Faransa. Ranar Jumma'ar dake tafe ne za a fara fafatwa, zuwa 11 ga watan Agustan da ke tafe. Tuni aka daukin matakan tsaro yayin da dubban masu aikin taimako ke ci gaba da gudanar da shirye-shiryen karshe, gabanin fara wannan wasannin da dubban 'yan wasa daga kasashen duniya za su halarta.
'Yan wasan kwallon kafa na kasa na Jamhuriyar NijarHoto: Getty Images/AFPHukumar Kula da Kwallon Kafa ta Jamhuriyar NIjar FENIFOOT ta fito da wani tsarin bunkasa wasanin kwallon kafa, inda ta dauki matakin koyi da wasu kasashe da aka samu ci-gaba a wasanin na kwallon kafa. An shirya wasanin da ake gudnarawa a yanzu haka a jihar Tahoua, wadanda suka hada wakilan jihohi guda takwas na kasar. Tuni dai masu sha'awar kwallon kafa a kasar suka nuna jin dadinsu da wannan gasa, koda yake a jihar Tahoua da ke zaman mai masaukin baki suna nuna takaicinsu sakamakon fitar da ita da aka yi daga gasar.