Tawagar kwallon kafar Ingila ta kai wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Turai bayan ta yi waje da takwararta na Netherlands.
Washington dc —Wasan da ya wakana a filin wasan Westfalenstadion na birnin Dortmund ya tashi ci 2-1 inda Xavi Simons ya farke wa Netherlands minti 7 da fara wasa.
Kyaftin din Ingila, Harry Kane, ta bugun da ga kai sai mai tsaron raga, ya zura wa Ingila a dai dai minti 18.
Bayan hutun rabin lokaci Ollie Watkins, wanda ya shigo wasan a minti 81, ya farke wa Ingila a minti na 90.
A jiya Talata, Tawagar kwallon kafar Sifaniya ta kai wasan karshe a gasar bayan ta ci Faransa 2-1 a filin wasa na Allianza Arena a birnin Munich na Kasar Jamus.
Sakamakon wasannin, Sifaniya da Ingila za su fafata ranar Lahadi 14 ga watan Yuli a wasan karshe wanda za a buga karfe 8 na dare agogon Najeriya da Nijar a filin wasa na Olympiastadion da ke birnin Berlin.