Dortmund ta yi rashin nasara a dukkannin wasannin da ta fafata guda hudu a wannan kaka tun daga farkon wannan shekara ta 2025. Kazalika kungiyar na fuskantar rashin tabbas a teburin wasannin Bundesliga na kasar Jamus inda take a matsayi na 10.
Karin bayani: Dortmund ta lallasa Freiburg da ci 4-0
Babban daraktan kungiyar Lars Ricken ya shaida wa manema labarai cewa suna matukar bukatar Nuri Sahin amma basu da zabi illah yin bankwana da shi sakamakon rashin nasarar da kungiyar ke fuskanta, duk da cewa Sahin ya cancanci yabo.
Karin bayani: Fatan Jamusawa bayan nasarar Dortmund
Hukumar gudanarwar kungiyar ta sanar da sunan Mike Tullberg a matsayin wanda zai jagoranci kungiyar kwallon kafar ta Borussia Dortmund gabanin karawar da kungiyar za ta yi da Werder Bremen a mako mai zuwa.