'Dan wasan Najeriya da Leverkusen ya tsallake rijiya da baya

'Dan wasan Super Eagles ta Najeriya da Bayer Leverkusen a nan Jamus Victor Boniface ya tsallake rijiya da baya, bayan gamuwa da wani mummunan hadarin mota a kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama na Frankfurt.

Karin bayani:Bayer Leverkusen ta kafa tarihi a kakar wasan Bundesliga

Sanarwar da kungiyarsa ta fitar a Lahadin nan ta ce Boniface ya je filin jirgin ne don dauko wani abokinsa, inda ya samu rauni kadan, amma motarsa ta yi raga-raga, kamar yadda 'dan wasan da kansa ya wallafa hotonta a shafukan sada zumunta, kafin daga bisani ya goge.

Karin bayani:Boniface ba zai buga wa Najeriya wasa a AFCON ba

A ranar Asabar Leverkusen ta doke Eintracht Frankfurt da ci 2-1, inda Boniface ya zura kwallo ta biyun da ta ba ta nasara, sannan ya barar da bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Kuma a bara ne kungiyar ta lashe gasar Bundesliga ta nan Jamus a karon farko a tarihinta.


News Source:   dw.com