Dan Kwallon Kafar Najeriya Abubakar Lawal Ya Fadi Ya Mutu A Uganda

Dan Kwallon Kafar Najeriya Abubakar Lawal Ya Fadi Ya Mutu A Uganda

A jiya Litinin, ‘yan sandan Uganda suka bayyana cewar suna gudanar da bincike a kan mutuwar dan wasan kwallon kafar Najeriya wanda ya fado daga farfajiyar benen wani kanti a birnin Kampala.

washinton dc — 

Dan wasan gaban mai shekaru 29 na buguwa kungiyar dake gasar firimiiyar Uganda mai suna Vipers wasa.

Ya fado daga bene na 3 na kantin Voicemall da safiyar jiya Litinin, a cewar sanarwar ‘yan sanda.

Ya jima yana ziyarar wata budurwarsa da ke zaune a wasu gidaje dake hade da kantin.

Budurwar ta shaidawa ‘yan sanda cewar ta barshi shi kadai jim kadan kafin fadowar.

A sanarwar da ta fitar, kungiyar kwallon kafa ta Vipers tace "muna matukar takaicin sanar da mutuwar da dan wasa, Abubakar Lawal, ya yi a yau da safe.

“Zuciyoyi da addu’o’imu na tare da iyalan Lawal da masoyansa na kungiyar da abokai da masoyansa a wannan lokaci na alhini,” a cewar sanarwar.

Lawal ya kasance dan wasan gaban kungiyar mai kai hari tun bayan daya koma cikin daga as Kigali ta Rwanda a watan Yulin 2022.


News Source:   VOA (voahausa.com)