Argentina, mai rike da kofin Copa America ta samu kai wa wasan karshe na gasar bayan da ‘yan wasanta Julian Alvarez da Lionel Messi su ka zura kwallaye 2-0 kan Kanada a wasan kusa da na karshe da su ka buga a New Jersey.
WASHINGTON D.C. —Tawagar ‘yan wasan Argentina za ta kara da Uruguay ko Colombia a wasan da za’a buga ranar Lahadi a Florida, wasan da ka iya zama na karshe ga manyan ‘yan wasan tawagar Argentina da su ka hada da Lionel Messi, Angel Di Maria da kuma Nicolas Otamendi.
Argentina ta lashe kofin Copa America sau 15 kuma ta kai wasan karshe sau shida a gasar da aka buga sau takwas da ta shige, amma Kanada ta tada hankali su a cikin minitina 20 na farkon wasan, inda Jacob Shaffelburg ya buga kwallo da karfi har sau biyu da a kusa shiga raga.
Bayan da aka takura su a farkon wasan, dan wasan Argentina Rodrogi De Paul ya bai wa Alvarez kwallo, wanda ya zura a miniti na 22 da fara wasan.
Argentina, wadda ta lashe gasar cin kofin duniya ta 2022, kuma ta daya a jadawalin Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA, a hankali ta karbe wasan, kuma Messi ya samu damar zura kwallo ta biyu a miniti na 51.
Kwallon ta sa Messi ya koma matsayi na biyar a jadawalin wadanda suka fi zura kwallo a gasar cin kofin Copa America, inda yake mataki daya da Paolo Guerrero na Peru da Eduardo Vargas na Chile, wadanda su ka zura kwallo 14.
Kwallon ta 109 ga Argentina kuma ta ba shi damar wuce dan wasan Iran Ali Daei na zama na biyu a jadawalin jerin wadanda su ka fi zura kwallaye na kasa da kasa.
Messi na biye da Cristiano Ronald ne, wanda ya zura kwallaye 130 ga Portugal.