Kungiyar kwallon kafa ta Najeriya ta ki fafatawa da Libya sakamakon tirjayar da tawagar suka fuskanta a filin jiragen saman Libyan a kan hanyarsu ta zuwa birnin Benghazi don wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin kasashen Afirka ta 2025.
Karin bayani: Najeriya ta kaurace wa gasar AFCON a Libya
Maki 3 da Najeriya ta samu zai bata damar kasance ta farko a saman teburin 'yan wasa na rukunin D, hakan na nufin wasanni biyu ke nan suka rage wa Najeriya domin kai wa ga matsayin da Benin ta ke da maki hudu da kuma Ruwanda da maki biyar.