An haifi Darboe a kasar Gambia kuma ya buga wasanni biyu a tawagar Amurka ta 'yan kasa da shekaru 17.
Washington D.C. —Bayern Munich ta sanya hannu kan dan wasan tsakiya mai kai farmaki, Bajung Darboe mai shekaru 18 wanda Ba’amurka ne.
Ta dauko shi ne daga kungiyar LAFC ta birnin Los Angeles California.
Bayern ta bayyana cewa Darboe ya sanya hannu kan “yarjejeniya mai tsawo” kuma zai shiga kungiyar ta matasa wacce ke kasar Jamus.
Darboe ya ce, “babban burina ya cika” ta hanyar shiga kungiyar Bayern.
An haifi Darboe a kasar Gambiya kuma ya buga wasanni biyu a tawagar Amurka ta 'yan kasa da shekaru 17. Haka kuma, ya buga wasa a ƙungiyoyin matasa na LAFC da Philadelphia Union.
Bayern da LAFC suna da hadin gwiwa mai fadi a karkashin alamar Red&Gold Football, wanda ke mai da hankali kan bunkasa matasan 'yan wasa.