Cikin wani yanayi mai cike da rudani, Beljiyam ta samu nasara a wasannin neman shiga gasar kwallon Tennis ta Davis Cup. Dan wasan kasar Chile Cristian Garin ne dai ya ki yadda ya ci gaba da wasa, bayan da suka yi karo da abokin karawarsa dan kasar ta Beljiyam Zizou Bergs da har ya kai shi kasa sai da likita ya duba shi. Ko da yake, likitan na musamman da ya duba shi ya ce zai iya ci gaba da wasan, amma Garin da tawagarsa suka ki amincewa. Bergs dai ya yi ta bai wa Garin hakuri, ya ma bai wa Kyaftin Chile hakuri yana mai cewa bai so abin ya kare a haka ba. Hukumar Kula da Wasannin Tennis din ta yanke hukuncin bai wa Bergs nasara da ci shida da uku da hudu da shida da kuma bakwai da biyar, abin da ya bai wa Beljiyam nasara ta samun cancantar halartar gasar ta Davis Cup.
Karin Bayani: Karawa tsakanin VfB Stuttgart da Borussia Mönchengladbach
Shugaban kasar Amurka na 47 wato Donald Trump ya sake darewa kan karagar mulki na tsawon shekaru hudu nan gaba, a daidai lokacin da Amurkan da hadin gwiwar kasashen Kanada da Mexico za su karbi bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a shekara mai zuwa ta 2026. Ko wanne irin tasiri gwamnatin Trump za ta iya yi a harkokin wasanni a alakarta da 'yan wasa musanman na cikin Amurkan da ma matakin da ya dauka a kan makwabtan nata a baya-bayannan?
Hausawa sukan ce Sarki goma zamani goma. Dawowar Trump gadon mulki a karo na biyu, tamkar ya bude wani sabon babi ne da zai shafi rukunin ‘yan wasa mata-maza, akalla tsawon shekaru hudu nan gaba, ko ma fiye da haka. Domin kuwa, yana hawa karagar mulki ya ayyana wata dokar kamar haka. Wannan mataki na Trump da ya janyo cece-kuce, bai zo wa wasu mutane da mamaki ba, duba da yadda gwamnatinsa ta dukufa, warware ko soke wasu daga cikin manufofin gwamnatin tsohon Shugaba Joe Biden, da kuma yadda ya ce a hukumance, gwamnatinsa jinsi biyu kawai ta sani; watau mace da namiji.
A gasar Premier League ta Ingila a karshen mako kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta karbi bakuncin Manchester City ta kuma yi mata dukan kawo wuka da ci dai-dai har biyar da daya. Tun dai a mintuna biyu da fara wasan ne, Arsenal ta zura kwallo a ragar City, inda bayan an dawo hutun rabin lokaci City din ta farke. Sai dai kuma tamkar ta kirawa kanta ruwan kwallaye, domin minti daya kacal bayan farke kwallon ne Arsenal ta kara mata ta kuma ci gaba da zura kwallo har a mintuna na karshe na wasan.
Ita ma takwarar City din wato Manchester United ta kwashi kashinta a hannu a gida da ci biyu da nema a hannun Crystal Palace, kana Liverpool ta bi Bounermouth har gida ta lallasa ta da ci biyu da nema. Newcastel ma ta sha kashi a gida da ci biyu da daya a hannun Fullham, yayin da Everton ta karbi bakuncin Leicester City ta kuma caskara ta da ci hudu da nema. Har yanzu dai Liverpool ce a saman tebur da maki 56 yayin da Arsenal ke mara mata baya a matsayi na biyu da maki 50. Sai Nottingham Forest a matsayi na uku da maki 47.
A gasar Bundesliga ta Jamus kuwa duk da cewa Borussia Dortmund ta yi abin kai a karshen mako ta hanyar yin nasara da ci biyu da daya a gidan Heidenheim, hakan bai hana ta ci gaba da zama daram a matsayi na 11 a teburin kakar lig din Jamus din ta bana ba. Ita kuwa Bayern Munichi da har yanzu take saman tebur, ta sha da kyar ne a gida a wasansu da Holstein Kiel da ta yi mata dan hakin da ka raina. Sai da Bayern din ta ci kwallaye hudu da nema kafin jaririyar kungiyar ta Kiel ta farke kwallaye uku cikin hudun da babbar yayan ta zura mata, abin da ya sanya aka tashi wasan bayern na da ci hudu Kiel din kuma uku.
A sauran wasannin da aka fafata a karshen mako a Bundesliga ta Jamus kuwa, Borussia Mönchengladbach ta bi Stuttgart har gida ta lallasa ta da ci biyu da daya. An dai tafi hutun rabin lokaci Mönchengladbach din na da ci daya Stuttgart na nema, sai dai bayan an dawo dan wasan Borussia Mönchengladbach din ya ci gida abin da ya sanya Stuttgart ta samu kwallo daya. Amma ana dab ta tashi daga wasan a mintuna na 81 Borussia Mönchengladbach din ta kara kwallo daya a ragar Stuttgart, abin da ya san ya aka tashai wasan Borussia Mönchengladbach na da ci biyu Stuttgart mai masaukin baki na da daya. Ga dai kadan daga cikin yadda wasan ya gudana.
Har yanzu dai Bayern Munich ce ke a saman tebur da maki 51, yayin da takwararta Bayer Leverkusen da ke rike da kambu ke matsayi na biyu da maki 45 sai Frankfurt a matsayi na uku da maki 38.
Kungiyoyin kwallon kafa na Arsenal da Aston Villa da Atlético de Madrid da Barcelona da Inter Mailand da Bayer Leverkusen da Lille da kuma Liverpool sun tsallake zuwa rukunin 'yan 16 a gasar cin kofin zakarun Turai, yayin da kungiyoyin da suka hadar da Borussia Dortmund da Bayern München da Juventus da Manchester City da Paris Saint-Germain da Real Madrid da Sporting CP ke da sauran aiki a gabansu na neman cancantar kai wa zagayen na 'yan 16 ta hanyar wasannin da za su fafata a mako mai zuwa.