An Zabi Troost-Ekong Da Lookman Domin Lashe Kyautar CAF Ta Bana

An Zabi Troost-Ekong Da Lookman Domin Lashe Kyautar CAF Ta Bana

Bikin mika kyautar ta CAF zai gudana ne a birnin Marrakech na kasar Morocco, a ranar 16 ga watan Disamba mai zuwa.

washington dc — 

An zabi jagoran tawagar Super Eagles, Williams Troost Ekong da dan wasan gabanta Ademola Lookman domin fafatawa a gasar lashe kyautar hukumar kwallon kafar afrika (CAF) ta bana, a ajin maza.

Zabin Lookman baya rasa nasaba da rawar daya taka a gasar cin kofin nahiyar Afrika ta bara, inda ya zura kwallaye 3 abin da ya baiwa Najeriya kaiwa wasan karshe na gasar da kuma bajintar daya nuna a wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar turai (Europa) ta bana.

Dan wasan mai shekaru 27 ya zura kwallaye 3 rigis a raga inda ya zamo dan wasa na farko a tarihi da yayi irin wannan bajinta a wasan karshe, sannan ya baiwa Atalanta damar kungiyar kwallon kafar turai ta farko da ta lashe gasar.

Troost, da aka ayyana a matsayin dan wasa mafi bajinta a gasar cin kofin nahiyar Afrika (AFCON) ta bara, ya jefa kwallaye 3 a gasar.

Bikin mika kyautar ta CAF zai gudana ne a birnin Marrakech na kasar Morocco, a ranar 16 ga watan Disamba mai zuwa.


News Source:   VOA (voahausa.com)