An Haramtawa Kociyan Liverpool Shiga Wasanni 2

An Haramtawa Kociyan Liverpool Shiga Wasanni 2

Kociyan Liverpool Arne Slot ba zai kasance a gefen layi a wasan da kungiyar za ta kara da Newcastle a gida ba bayan da aka haramta masa shiga wasanni 2 tare da cin sa tara mai nauyi saboda halayyar daya nuna a fafatawarsu ta Merseyside.

washington dc — 

Kwallon da James Tarkowski ya farkewa Everton ana daf da busa tashi a gasar da aka tashi kunnen doki ci 2-2 a ranar 12 ga watan Fabrairun da muke ciki ce ta haddasa hatsaniyar.

Alkalin wasa ya kori Arne Slot da mataimakinsa Sipke Hulshof tare da Curtis Jones na Liverpool da dan wasan tsakiyar Everton Abdoulaye Doucoure daga filin.

Hukumar kwallon kafar Ingila (FA) ta fitar da sanarwa a yau Laraba tana cewa wata hukumar ladabtarwa mai zaman kanta ta hukunta kungiyoyin kwallon kafar Everton da Liverpool da kuma Slot da Hulshoff.


News Source:   VOA (voahausa.com)