An Dakatar Da Mudryk Na Chelsea Sakamakon Gaza Tsallake Gwajin Amfani Da Kwayoyi

An Dakatar Da Mudryk Na Chelsea Sakamakon Gaza Tsallake Gwajin Amfani Da Kwayoyi
washington dc — 

Dan wasan gaban Chelsea Mykhailo Mudryk ya gaza tsallake gwajin amfani da kwayoyin kara kuzari, a cewar kungiyar da ke buga gasar Firimiya a yau Talata, kamar yadda rahotanni suka bayyana an yi wa dan asalin ukraine din dakatarwar wucin gadi.

Chelsea tace kungiyar kwallon kafar ta sanar da ita game da mummunan sakamakon da aka gano a cikin samfurin fitsarin da dan wasan gefen mai shekaru 23 ya bayar.

Mudryk ya koma Chelsea daga kungiyar Shakhtar Donestsk a watan Janairun 2023 a kan dala miliyan 112.

Hukumar yaki da shan kwayoyin kara kuzari ta burtaniya (UKAD) ta gargadi ‘yan wasa a shafinta na yanar gizo cewar zasu fuskanci dakatarwar shekaru 4 matukar ta gano suna amfani da wata kwaya da aka haramta da gangan.

Idan karya dokar ta shafi wata takamaimiyar kwaya ko wani gurbataccen magani, kuma dan wasan ya iya gamsar da cewa bashi da laifi, hukuncin na iya tashi daga dakatarwar shekaru 2 zuwa nuna rashin gamsuwa, duba da girman laifin.


News Source:   VOA (voahausa.com)