An Bayyana Sunan Sam Vincent A Matsayin Daraktan Gasar BAL Ta Bana

An Bayyana Sunan Sam Vincent A Matsayin Daraktan Gasar BAL Ta Bana

Matasan 'yan wasa da suka fito daga Afirka da Turai da Amurka da sauran kasashe fiye da 30 zasu fafata a wasannin sharar fagen na kwanaki 3, wadanda zasu gudana a dakin wasanni na Ibn Yassine.

washington dc — 

A yau Talata hukumar shirya gasar kwallon kwando ta Afirka (BAL) ta bayyana sunan zakaran kwallon kwando Amurka (NBA) Sam Vincent Camp, a matsayin daraktan hadaddiyar gasar kwallon kwandon nahiyar Afirka ta 2025, da za ta gudana daga ranar Juma'a 10 zuwa Lahadi 12 ga watan Janairun da muke ciki, a birnin Rabat na kasar Morocco.

Matasan 'yan wasa da suka fito daga Afirka da Turai da Amurka da sauran kasashe fiye da 30 zasu fafata a wasannin sharar fagen na kwanaki 3, wadanda zasu gudana a dakin wasanni na Ibn Yassine.

"Muna farin ciki da Sam Vincent Camp ya shigo cikinmu a matsayin daraktan sansanin daukar horon wasan kwallon kwando ta Afirka gabanin karo na 5 na wannan muhimmiyar gasa," kamar yadda shugaban shirya gasar kwallon kwando ta Afirka Amadou Gallo Fall ya bayyana.

A zaman da ya yi a NBA, Vincent Camp ya bugawa kungiyoyin kwallon kwando irinsu Boston Celtics da Seattle Supersonics da Chicago Bulls da Orlando Magic wasa.

A shekarar 1992, Vincent ya rungumi aikin horas da 'yan wasa, inda ya horas da kungiyoyin kwallon kwandon kasashe da dama a nahiyoyin Afirka, Asiya da kuma Turai.

A yayin gasar wasannin Olympics da ta gudana a birnin Athens, ya horas da tawagar Najeriya ta mata, wacce ta yi galaba a kan takwararta ta Koriya ta Kudu wacce ta zamo irinta ta farko da wata kasar Afirka ta samu a gasar Olympics a wasannin kwallon kwandon mata.

Shekaru 2 bayan hakan, Vincent ya jagoranci tawagar Najeriya ta maza zuwa zagaye na 2 na gasar kwallon kwandon duniya ta 2006 da hukumar shirya gasar kwallon kwandon duniya (FIBA) ke shiryawa.


News Source:   VOA (voahausa.com)