AFCON 2025: Najeriya Ta Fitar Da Jerin ‘Yan Wasan Da Za Su Kara Da Benin, Rwanda

AFCON 2025: Najeriya Ta Fitar Da Jerin ‘Yan Wasan Da Za Su Kara Da Benin, Rwanda

Fitar da sunayen ‘yan wasan na zuwa ne kwana guda bayan da aka nada Bruno Labbadio a mstayin sabon kocin kungiyar ta Super Eagles.

Washington D.C. — 

Najeriya ta fitar da tawagar ‘yan wasan da za su kara a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi badi.

Shafin kungiyarta Super Eagles ne ya fitar da sunayen ‘yan wasa 23 a ranar Laraba.

Najeriya za ta kara da Benin a ranar 7 ga watan Satumba a birnin Uyo, sai kuma a ranar 10 ga watan Satumba ta dangana zuwa Kigali domin karawa da Rwanda.

Fitar da sunayen ‘yan wasan na zuwa ne kwana guda bayan da aka nada Bruno Labbadio a matsayin sabon kocin kungiyar ta Super Eagles.

Wadannan wasanni za zamanto kazaran gwajin dafi ga Labbadia wanda ya maye gurbin Finidi George.

Najeriya ce ta zo ta biyu a gasar AFCON da ta shude yayin da Ivory Coast da ta karbi bakuncin gasar ta lashe kofin bayan ta ci Najeriya da ci 2-1.

Sau uku Najeriya na lashe kofin gasar ta AFCON, lokacin na karshe shi ne a shekarar 2013 a Afirka ta Kudu.

Ta kuma lashe kofin a shekarar 1994 a Tunisia sai kuma a shekarar 1980 inda ta karbi bakuncin gasar.

Ga jerin ‘yan wasan dna Super Eagles:

Masu tsaron raga: Stanley Nwabali, Maduka Okoye, Amas Obasogie.

Masu tsaron gida: William Troost-Ekong, Bright Osayi-Samuel, Olisa Ndah, Bruno Onyemaechi, Oluwasemilogo Ajayi, Calvin Bassey, Olaoluwa Aina.

‘Yan wasan tsakiya: Wilfred Ndidi, Raphael Onyedika, Alhassan Yusuf Abdullahi, Fisayo Dele-Bashiru, Frank Onyeka, Alex Iwobi.

‘Yan wasan gaba: Samuel Chukwueze, Victor Osimhen, Kelechi Iheanacho, Victor Boniface, Moses Simon, Ademola Lookman, Taiwo Awoniyi.


News Source:   VOA (voahausa.com)