Najeriya ita ce ta shida a iya taka kwallo a nahiyar Afirka yayin da Libya take matsayi na 33.
Washington D.C. —A hukumance, an fitar da ranakun da kungiyar ‘yan wasan Najeriya ta Super Eagles za ta kara da ta Libya a wasannin neman shiga gurbin gasar AFCON ta 2025.
Super Eagles za su karbi bakuncin wasan farko a ranar 11 ga Oktoba a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom.
Kwanaki hudu bayan wannan karawa kungiyoyin za su sake haduwa a Tripoli.
Super Eagles ce ke jagorantar Rukunin D da maki hudu bayan nasara ta 3-0 a gida akan Benin da kuma canjaras da suka yi da Rwanda a Kigali.
Libya tana rike da matsayi na karshe a cikin rukunin tare da maki guda daga adadin wasanni biyu da ta buga.
Najeriya ita ce ta shida a iya taka kwallo a nahiyar Afirka yayin da Libya take matsayi na 33.