Lookman wanda ke taka leda a kungiyar Atalanta dake buga gasar Serie A ta kasar Italiya ya dauki hankula bayan da ya zura kwallaye 3 a wasan karshe na gasar Europa wacce kulob din nasa ya lashe.
washington dc —Dan wasan Najeriya da ya yi fice a kungiyar Atalanta a gasar Serie A na Italiya Ademola Lookman, ya lashe kyautar lambar yabo ta CAF na shekarar 2024, yayin bikin karrama ‘yan wasa da hukumar kwallon kafar Afirka ta shirya wanda ya gudana a ranar Litinin, 16 ga watan Disamba a birnin Marrakech na kasar Morocco.
Lookman wanda ke taka leda a kungiyar Atalanta dake buga gasar Serie A ta kasar Italiya ya dauki hankula bayan daya zura kwallaye 3 rigis a wasan karshe na gasar Europa wacce kulob din nasa ya lashe.
Lookman ya yi takara tare da Simon Adingra (da ke bugawa kasar Ivory Coast da kungiyar Brighton da Hove Albion wasa) da Serhou Gulrassy (da ke bugawa kasar Guinea da kungiyar Borussia Dortmund wasa) da Achraf Hakimi (da ke bugawa kasar Morocco da kungiyar PSG wasa).
A fannin mata kuma Babra Banda ta Zambia ce ta lashe gwarzuwar kwallon kafa ta Afirka ta 2024.