Zumar Centaury mafi tsada a duniya

Zumar Centaury mafi tsada a duniya

Zumar Centaury da aka tattara a wani kogo da ke nesa da jama’a wanda ke a wajen da ya ke da tudun mita dubu 2,500 sama da ruwan teku, an sayar da kilo dayan ta kan kudi har Yuro dubu 10 wanda hakan ya sanya ta zama mafi tsada a duniya da kuma shiga littafin adana Fiyayyun Abubuwa Masu Ban Mamaki na ‘Guinness Book of Record’.

A bangarori masu tudu na yankunan Bahar Rum da Tekun Maliya da ke Turkiyya ake noma ciyawar Centaury ruwan dorawa, ita ce me samar da zuma mafi tsada a duniya. A kiwon zuma, ana diban ta sau 2 zuwa 3 a shekara, amma ta Centaury sau 1 kawai ake diban ruwanta a shekara. Ta bambanta sosai da ruwan zumar da aka sani. Tana da turarren kala, tana da dandano mai yaji-yaji kuma tana da adadi mai yawa na sinadaran magnesium, potasium, fenol, flavanoid da antioxidan. Malaman kimiyya na Turkiyya da aka aika musu zumar, sun yi gwajin tabbatar da ingancinta .


 


News Source:   ()