Zimbabwe ta gaza karbar alluran riga-kafin Corona miliyan 3 saboda rashin wajen ajiya

Zimbabwe ta gaza karbar alluran riga-kafin Corona miliyan 3 saboda rashin wajen ajiya

Sakamakon rashin wajen ajiya, Zimbabwe ta ki amincewa da karbar alluran riga-kafin cutar Corona kwaya miliyan 3 na kamfanin Johnson&Johnson da Tarayyar Afirka za ta aika mata a matsayin tallafi.

A wasikar da Ma'aikatar Kudi ta aikawa Bankin Shiga da Fitar da Kayyaki na Afirka an bayyana cewa, saboda rashin wajen ajiya, Zimbabwe ba za ta karbi allurar riga-kafin Corona guda miliyan 3 da Tarayyar Afirka ta ba ta taimako ba wanda aka shirya kaiwa kasar a watan Agusta mai zuwa.

Wasikar ta kuma ce, gwamnatin Zimbabwe na tsoron irin illar da ake tunanin allurar na da ita.

A yanzu Zimbabwe na amfani da alluran riga-kafin Corona na Sinovac ta China da Sputnik V ta Rasha.


News Source:   ()