Mutane 5 sun rasa rayukansu sakamakon zaftarewar kasa a wata mahakar ma'adanan jihar Sulawesi ta Tsakiya da ke kasar Indonesiya.
Tashar talabijin ta Metro ta sanar da cewa, an samu ruftawar kasa a mahakar ma'adanan zinare ba bisa ka'ida ba da ke yankin Parigi Moutong.
Mahukunta sun ce, an ciro jikkunan mutane 5, yayin aka kubutar da wasu 6.
Ana ci gaba da aiyukan kubutar da mutane daga ibtila'in.
A ranar 26 ga watan Fabrairun 2019 ma an samu zaftarewar kasa a mahakar ma'adanan zinare ba bisa ka'ida ba a yankin Bolaang Mongondow da ke jihar Sulawesi ta Tsakiya. Mutane 27 ne suka mutu a lamarin.
News Source: ()