Mutane 20 sun bata, wasu 14 sun jikkata sakamakon zaftarewar kasar da mamakon ruwan sama ya janyo a yankin Nganjuk na jihar Java ta Gabas da ke Indonesiya.
Shugaban Sashen Sadarwa na Hukumar Yaki da Ibtila'o'i, Raditya Jati ya shaida cewar, a kauyen Ngetos na yankin Nganjuk gidaje 8 sun lalace.
Jati ya sanar da batan mutane 20 tare da jikkatar wasu 14 sakamakon zaftarewar kasar, ana kuma ci gaba da neman wadanda suka bata tare da kwashe mutanen yankin.
Jati ya kara da cewa, sakamakon mamakon ruwan saman da aka samu a yankin Pasuruan na jihar Java ta Gabas, iyalai 294 sun illatu.
Indonesiya da ke kan layin Equador, na yawan fuskantar mamakon ruwan sama a tsakanin watannin Oktoba da Afrilu.