Wasu abubuwa sun fashe a Yukren

Wasu abubuwa sun fashe a Yukren

Wasu sinadarai sun fashe a wata masana'anta da ke garin Rivne na kasar Yukren.

Bayanan farko da aka fitar sun bayyana cewa, babu wanda ya jikkata sakamakon lamarin, amma hayaki ya turnuke sama bayan fashewar.

An bayyana cewa, fashewar ta afku bayan da aka danna wani waje a jikin bututun iskar gas.

Hayaki ruwan goro ya turnuke sama inda aka bayyana ba ya wata barazana ga rayuwar jama'a.

An kwashe ma'aikatan masana'antar tare da fara gudanar da bincike.

 


News Source:   ()