Wasu abubuwa sun fashe a cikin tekun Hazar daga bangaren gabar Baku babban birnin Azabaijan.
Shafukan yanar gizo sun yada bidiyon wuta da hasken da suka kama a lokacin da fashewar ta afku.
Kakakin kamfanin Man Fetur na Kasa na Azabaijan (SOCAR) Ibrahim Ahmedov ya shaida cewa, babu wani abu mallakar kamfanin da ya yi bindiga a teku.
An samu labarin cewa, mahukuntan sashen makamashi sun bayyana cewar, wani jirgin ruwa a yankin Umit Gas ne ya yi bindigar.
News Source: ()